A watan Yuli, wani jami’in hukumar makamashi na Rasha ya ziyarci Jamhuriyar Nijar don sanya hannu kan yarjejeniyar inganta makashi tsakanin kasashen biyu.
Yarjejeniyar ta tsara hanyoyin da kasashen biyu za su iya hadaka a bangaren wutar lantarki da magunguna da horar da ma’aikata.
- Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?
- Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Wannan ya nuna cewa Rasha na kara kutsawa cikin kasar, wadda ke cikin wadanda suka fi yawan ma’adanin yureniyom (uranium) a duniya, da ma sauran kasashen yankin Sahel a nahiyar ta Afirka.
Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu.
Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin taimakon kasashen da makamai da horo.
Amma ganin yadda har yanzu kasashen ke ci gaba da fuskantar hare-hare, shin za a iya cewa alaka da Rasha ta yi musu rana?
Sababbin kawayen Moscow
Tun a 2021 Rasha ke tura dubban sojoji da makaman da suka kai miliyoyin Dala zuwa Mali da Burkina Faso da Nijar.
Tana haka ne domin taimakon kasashen wajen yaki da matsalolin tsaro da ya dabaibaye yankin Sahel, inda kungiyoyin ‘yanbindiga masu ikirarin jihadi ke amfani da raunin gwamnati da talauci da kiyayyar gwamnatotin kasashen yamma da rikice-rikicen kabilanci a kasashen wajen kutsawa.
Sojojin hayar na Rasha sai suka samu shiga, inda gwamntocin soji a kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka rika daga tutar Rasha a tarukansu, wanda hakan ke nuna goyon bayansu da agajin Rasha.
Hakan ya sa kasashen uku suka nisanta kansu daga Faransa, wadda ita ce ta raine su a baya, da ma wasu kasashen na yamma.
Ba kamar sauran kasashen na yamma ba, ita Rasha ta tura musu dakaru da makamai ba tare da wasu sharuda ba, wanda a lokuta da dama ke zuwa da alkawarin tabbatar da mulkin dimokuradiyya.
Dakarun Wagner na Rasha sun isa Mali ne a 2021 bayan sojojin Faransa sun fice daga kasar, inda a shekarar 2023 sojojin Mali tare da taimakon dakarun Wagner suka kwace wani babban sansanin ‘yanwataye da ke arewacin kasar.
Amma tun bayan wannan nasarar, hare-haren kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal Muslimin (JNIM) mai alaka da al-Kaeda sai suka karu.
A 2024, sama da mutum 70 ne suka rasu, sannan sama da 200 suka ji rauni a harin JNIM a babban birnin Mali, Bamako.
“Zuwan dakarun Wagner bai dakile harkokin kungiyar JNIM ba,” a cewar Hani Nsaibia ta kungiyar ACLED.
A 2023 ne Yebgeny Prigozhin, jagoran Wagner ya rasu a hadarin jirgin sama kwanaki kadan bayan ya yi yunkurin kifar da gwamnatin Bladimir Putin a Rasha.
Sai gwamnatin Rasha ta yi wa dakarun garambawul, sai suka koma dakarun Afirka wato Africa Corps.
A watan Yunin bana ne dakarun na Wagner suka sanar da ficewarsu daga Mali, inda suka ce sun kammala aikin da ya kawo su.
A wani sako da suka fitar a Telegram, sun ce sun “kashe dubban ‘yantawaye da shugabanninsu da suka dade suna addabar fararen hula.”
Ci gaba da rikice-rikice
Kamar yadda alkaluman Global Terrorism Inded suka nuna, sun ce yankin Sahel ne “cibiyar ta’addanci” na duniya, kuma a yankin ne aka samu kusan rabin mutuwa da k da alaka da ta’addanci a duniya, wanda ya sa ake tambayar amfanin shigar Rasha cikin lamarin.
Haka kuma gabashin Mali da Burkina Faso sun dade suna fama da matsalar tsaro tun wajajen 2025.
ACLED ta ce an kashe sama da mutum 20,000, sannan sama da miliyan sun rabu da muhallansu.
A Nijar, akwai gomman sojojin Rasha da suke aiki tare da sojojin kasar, amma har yanzu babu wata nasarar a-zo-a-gani.
A watan Maris na bana, an kashe sama da mutum 40 a wani hari da aka kai a masallaci a yammacin Nijar.
Masanin tsaro Adib Saani ya ce mayakan Nijar da Mali da Burkina Faso sun kara kaimi ne saboda ficewar kasashen yamma.
Andre Lebobich, wani mai bincike a cibiyar Clingendael Institute da ke Netherlands, ya ce sojojin Rasha da ke yankin Sahel aiki ya musu yawa, wanda hakan ne ma a cewarsa ya sa JNIM suka fadada zuwa ksashen Togo da Benin.
Rashin karfin soji
Kwararre a fannin tsaro a Yammacin Afirka Hani Nsaibia ya ce sojojin Rasha da ke aiki a yankin Sahel sun yi karanci, wanda hakan ya sa yake ganin ba sa samun nasara.
Rahotanni sun ce an janye wasu sojojin Rasha saboda yakin Ukraine, wanda hakan ya haifar da gibi saboda babu sojojin wanzar da zaman lafiya daga kasashen yamma ba.
“Zai yi wahala sojojin Rasha 2,000 su iya maye gurbin sojojin wanzar da zaman lafiya kimanin 18,000 da ke aiki a yankin a baya,” in ji shi.
A wani taron tsaro a watan jiya, ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Labrob ya nanata cewa kasar za ta ci gaba da taimakon kasashen Afirka domin wanzar da zaman lafiya.
Amma masana na ganin magana kawai ba za ta iya wadatar ba, “domin mutanen yankin da dama suna rayuwa ne a kullum a kasa da dala, ga kuma rashin ababen more rayuwa,” in ji masanin tsaron Ghana, Adib Saani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp