Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Eric Chelle ya gayyaci tsohon dan wasan gaba na CSKA Moscow da Leicester City kuma kyaftin din tawagar kasar domin buga gasar cin kofin Unity Cup da za a yi a Landan a karshen watan nan, hakan na nufin bayan shekara daya Musa ya sake dawowa cikin tawagar Nijeriya domin buga wasa.
Tauraron dan kwallon dake taka leda a Kano Pillars a yanzu, ya kasance cikin jerin ‘yan wasa 25 da suka hada da ‘yan wasa 10 da ke kwallo a gida Nijeriya, da Chelle ya gayyata domin wakiltar kasar a gasar Unity Cup da zata kunshi kasashe daban daban na Turai da Afirika.
- Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan
- Sin Ta Soki Yunkurin Amurka Na Hana Amfani Da Chips Kirar Kasar Sin
Musa, wanda shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya kuma kyaftin din tawagar, ya dawo cikin tawagar a karon farko tun bayan da Super Eagles ta samu kyautar Azurfa a gasar cin kofin Afrika (AFCON) a farkon shekarar da ta gabata.
Duk da cewar bai buga wasa ko daya a gasar AFCON da ta gabata ba, wannan karon ana saran Musa zai kasance daga cikin wadanda zasu haska a gasar ta Unity Cup da kasashe zasu buga a Landan.
Za a gudanar da gasar cin kofin Unity Cup wanda ya kunshi Nijeriya, Jamaica, Ghana da kuma Trinidad and Tobago a filin wasa na Gtech Community mai daukar yan kallo 17,250 da ke Brentford a yammacin Landan, za a fara gasar ne da wasan kusa da na karshe a ranar Talata 27 ga watan Mayu, yayin da Trinidad & Tobago za ta kara da Jamaica, Washegari Nijeriya mai rike da kofin Afirka sau uku za ta fafata da Ghana mai rike da kofin Afirka sau hudu a wasan dab da na kusa da na karshe, wanda ake hasashen zai sake kulla gabar kwallo wadda aka shafe tsawon shekaru 74 anayi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp