Haramta shiga da manja da dangoginsa da kasar Indonesiya ta yi zuwa cikin kasar, musamman ganin cewa, kasar ce ke kan gaba a duniya wajen samar da shi, matakin nata ya zama wajibi ya zama darasi ga masu zuba jari a fannin da kuma yadda Nijeriya ke hankoron fitar da nata Manjan zuwa kasuwar duniya.
Kafin wannan matakin na haramtawar da kuma Manjan da aka sarrafa shi, Manjan ya kasance a kan gaba wajen samarwa Asiya kudaden musaya na kasar waje.
A watan Afirilun 2020, tan dinsa na samar wa da Indonesiya kimanin Dala 545, inda bayan shekaru biyu,ya haura zuwa Dala 1,700.Akasarin masana a fannin aikin noma sun bayyana takaicinsu, musamman duba a Jamhuriya ta daya ne, Asiya a karonta na farko ta zo Nijeriya ta dauki irin na kwakwar manja, amma abin takaici, a yau Indonesiya ta yi wa Nijeriya fintinkau wajen noman kwakwar manja da sarrafa ta.
Sai dai, Nijeriya ganin irin mahimmancin da fannin noma yake da shi, ta samar da tsari don kara habaka fannin, musamman don kara bunkasa nomanta domin kara bunkasa tattalin kasar da kuma kara samarwa da kanta kudaden shiga na waje.
Misali, duba ga wannan fashin baki da aka zayyano, idan aka yi dubi a kan tsarin da Babban Bankin Nijeriya CBN ya kirkiro da tsarin don a farfado da fannin abu ne da za a iya cewa Nijeriya ta farga.
Tabbas, a kasuwar duniya ana bukatar ta matuka, masana na gamin cewa, an fi samun riba mai yawa a fannin fiye da a fannin samar da manfetur da iskar gas.
A bayyana ne yake a yanzu gangar manja ta fi ta gangar danyen mai tsada.Ana yin nomanta ne na dogon zango saboda tsawon. tsawon lokacin da take zauka kafin ta kammala girma, sabanin sauran amfanin gona.
Saboda haka ne mahukunta na yanzu a CBN suka yunkuro don su sake dawo martabar fannin a matsayin wanda za a iya amfani da shi, don a kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Bugu da kari, CBN ya zabo fannin a matsayin daya daga cikin fanonin da zai amfana da daukin tsarin da ya kirkiro da shi.
Ya na da kyau a sani cewa, kafin Nijeriya ta samu ‘yancin kanta daga gun Turawar muljin mallaka, noman Kwakwar ya taka muhimiyyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin Yammacin kasar nan.
An kiyasta cewa, gibin da ake da shi, na manja ya kai mitrik tan 1,250,000 inda kuma bukatar da ake da ita ta man a cikin kasar nan ta kai ta kimanin metirik tan 2,500,000 wanda kuma a kasar, ana noma metirik tan 1,250,000 kacal.
Har ila yau, CBN ya kuma mayar da hankali wajen sake farfado da fannin ta hanyar zuba kudade da samar da kayan aiki a Kudancin Nijeriya, musamman a Kudu Maso Gabas.
Daukin na CBN a fannin an yi ne don a kara yawan noman Kwakwar Manja
daga metirikw tan 1,250,000 zuwa metirik tan 2,500,000 nan da 2028 ta hanyar noma akalla, kadada 350,000 Babbar manufar da ake son cim ma a fannin shi ne, a samar da wadataccen manjan da dangoginsa a kasar nan tare da kuma samar da ingantaccen sa, kara samar da kudaden shiga ga Asusun ajiya na kasar da ke a ketare.
Kara bunkasa kwarewa dabarun noman Kwakwar Manja ‘yan Nijeriya, samarwa wadanda ke a fannin saukin samun rancen kudaden, samar da tallafi ga manya kananan sana’io domin a kara habaka tattalin arzikin kasar nan.
A yanzu haka, ana kan tartaunawa da wasu jihohin da fannin ya durkushe a jihohin su kamar aikin na noman Kwakwar Manja da ake kira da Adapalm da ke a Kudu maso gabas tare da nemo masu ruwa da tsaki a fannin, inda ya zuwa yanzu, an kebe kadada 170,000 ga masu son zuba jari a jihohi 11.
Misali, Godwin Emefiele a 2019 ya kaddamar da shirin nomanta na (ESOPP), wanda yake ci gaba da fadada, inda a yanzu gwamnatin jihar ta kebe jimlar kadada 65,000 ga masu son zuba jarinsu a fannin.
Hakazalika, CBN ya zuba naira biliyan 51.29 a cikin ayyukan a jihar, inda kuma jihar ta Ondo ta kaddamar da ayyukin da ta yiwa lakabi da Red Gold Project.
Bugu da kari, jihar ta kuma kebe filin yin nomanta ga kamfani tare da tallafawa kananan manoman na Kwakwar Manja da ya kai jimlar kadada 54,000, musamman domin a noma jimlar kadada 6,000,inda tuni, manomanta suka Har ila yau, sauran jihohin na ci gaba da tattaunawa da CBN ta hanyar bankunan su ma ajiya wato na (DMBs), musamman domin a taimaka wa kananan manoman da ke a cikin fannin.
Tuni dai, wadanda ke Sa idok a fannin suka fara yin hasashen cewa, a 2022 da kuma bayanta, ana sa ran za a noma kadada 350,000 wacce kuma za a noma su a 2028.
Tun bayan da CBN ya kirkiro da tsarin, ya amince tare da kuma turawa manya, matsakaita da kanana a fannin naira biliyan 73.38 .
Yana zama dole a sanar da cewa, kara cigaban da Indonesiya ke samu a fannin ne ya kara bai wa Emefiele kwarin gwiwar yunkuri sake farfado da fannin a kasarnankwararru sun kuma yi kira ga masu son zuba jari a fannin a kasar nan kar su bari wannan damar ta kubuce masu, musamman ganin cewa, alfanun da za a samu, bai sa iyakaBanda wannan bangaren na noman kwakwar manja, akwai kuma yunkurin da ake yi don a kara habaka fannin aikin Man Gyada a kasar nan.
Amadi Manomin kwakwar manja ne da ke zaune a garin Owerri.