Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Kokarin Inganta Magungunan Gargajiya Babbar Nasara Ce

by
3 years ago
in Kowa Ya Bar Gida ...
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daya daga cikin hanyoyin da al’umma ke kai wag a samun nasara ita ce, inganta abubuwan da suka taso suka tarar iyayensu da kakanninsu na yi, wato abubuwa irin na gargajiya, musamman wadanda ake amfani das u yau da kullum.

Maganin gargajiya na daga cikin abubuwan da al’umma ke gada, kuma suke ci gaba da amfani da shi a rauwarsu ta yau da kullum domin waraka ko ma riga-kafi.

Don haka ne ma al’ummar Hausa suka tashi tsaye wajen ganin sun inganta wannan fannin na mahganin gargajiya. Zuwa yanzu za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu domin kuwa kullum ana kara samun ci gaba a wannan fanni kuma ana tankade da rairaya ga masu yin sana’ar yadda ake tace bata-gari daga cikinsu.

Labarai Masu Nasaba

Allah Sarki Talaka!

Zabar Nanono Ministan Gona: Harkar Noma Za ta Kara Habaka A Nijeriya—Faruk

Zuwa yanzu akwai masu maganin gargajiyar da kullum suke bunkasa iliminsu na magani ta hanyar zamani, wadanda kuma tan an ne suke gano muhimman abubuwa da ke kawowa sana’ar ta su ci gaba da kuma kara ingantata.

Yanzu haka, an samu ci gaban zamani ta hanyar adana magungunan na gargajiya, kamar yadda ake adana sauran magunguna. Haka kuma yumkurin da gwamnati ke yi na samar da fannin koyar da ilimin magungunan gargajiya a jami’o’in Nijeriya, da nufin sanya harkokin magungunan na gargajiya su rinka tafiya daidai da zamani, zai taimaka wajen bunkasa maganin gargajiyar.

Rahotanni na nuni da cewa Ma’aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa dukkanin shiri ya kammala wajen ganin an kai ga fara koyar da darussa kan ilimin magungunan gargajiya a jami’o’in da ke fadin Najeriya, da nufin ganin cewar masu magungunan gargajiyar sun bi sahun tsarin kula da harkokin lafiya na zamani da ke da bukatar gudanar da bincike kan cututtuka kafin ba da magani, domin yin hakan zai sa a tabbatar da ka’idar amfani da maganin da za a bayar.

Gwamnatin ta Nijeriya dai ta bayyana hakan ne a wani taron kungiyar masu ruwa da tsaki a harkokin kula da lafiya a kasar. Taron ya kuma tabbatar da cewar kafin a cim ma kudirin samar da ingantacciyar lafiya ga jama’a, to dole ne a samu hadin kan masu magungunan gargajiya da ke kasar. To kun ga wannan babbar nasara ce ga masu wannanan sana’a ta maganin gargajiya, domin hakan zai sa gwamnati ta shigo cikin harkar, sannan ta bayara da gudummowa wajen bunkasa sana’ar.

Sai dai duk da haka, ma’aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya ta nunar a gurin taron cewar, hadin kai da masu ba da magungunan gargajiya shi ne kawai a ilimantar da su hanyar kula da lafiya a zamanance, ta yadda dole a karantar da su ilimin sanin jikin mutum da kimiyyar magunguna da cututtuka da sauransu.

Manufar da ake son cim ma wa

Dakta Abubakar Sakkwato Muhammad na daya daga wadanda suka gabatar da bayani a gurin taron, ya wayar da kan mahalarta taron kan manufar da ake bukatar a son cim ma wa.

“Tsarin kiwon lafiyarmu a Nijeriya na wanda Turawa suka shigo da shi ne, amma saboda tsadarsa mafi yawancin talakawanmu ba su da kudin biyan yadda za su samun wannan kiwon lafiya, shi ya sa suke zuwa wurin na gargajiya. Sauran kasashen duniya ma suna aiki da na gargajiyar, amma ana son shi ma ya bi kyakkyawan tsari na zamani, musamman wajen bada magani da kuma binciken lafiya kafin a bada maganin.”

Wani daga cikin masu bayar da maganin gargajiya da aka zanta da shi cewa ya yi “Jama’a na raja’a kan magungunan na gargajiya da yadda wani magani daya tilo ke maganin cututtuka daban-daban, sannan kuma ga sauki ga shi kuma ma fi kusa da mara lafiya. Saboda shi ma ya yi maraba da wannan kokari na inganta wannan sana’ a ta su ta bayar da maganin gargajiya, kuma ya tabbatar da cewa, wannan yunkuri zai taimaka musu kwarai da gaske.

Ci gaba a kokarin inganta kiwon lafiya

Dakta Nura Sani, malamin jami’a ne a Nijeriya da ke koyar da fannin ilimin Biochemistry, ya bayyana shawararsa kan yadda za a samu nasarar abin da ake son cim ma wa da kuma irin ci gaban da ake samu a kasar.

“Idan aka yi kyakkyawar fadakarwa, jama’a za su yarda su ba da hadin kai. Misali kamr mu nan  a Kano mun fara wannan shiri na inganta harkokin magungunan gargajiya. Sannan a duk lokacin da za a yi taro kan magungunan gargajiya a Jami’ar Ahmadu Bello ana gayyato sarakunan masu magungunan gargajiya domin su zo su baje kolin magungunansu. Ana samun tattaunawa da fahimtar juna.” Saboda haka wannan dama da masu maganin ke samu na kara musu karfin gwiwar bayar da hadin kan lalubo bakin zaren matsalolin day a dade da bacewa.

Yanzu dai ta tabbata cewar akwai tsananin bukatar da jami’an kula da harkokin lafiya din a gargajiyance da su rungumi tsarin na zamani don a samu tsafta a harkokin kula da lafiya a kasar.

Babban dai kalubale shi ne yadda za a cim ma yarjejeniyar samun sirrin magungunan da masu magungunan na gargajiya ke tattare da su.

Domin kuwa kullum fargabar da suke ita ce, kada bayan sai an gama cin moriyar ganga sannan a ce za a yard a kwauren.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Amfanin Ganyen Mangwaro A Jikin Dan’adam

Next Post

Yawan Karanta Littattafan Hausa Ya Sa Ni Sha’awar Rubuta Littafi — Rahmatu

Labarai Masu Nasaba

Talaka

Allah Sarki Talaka!

by
1 year ago
0

...

Zabar Nanono Ministan Gona: Harkar Noma Za ta Kara Habaka A Nijeriya—Faruk

by
3 years ago
0

...

Aljanin Da Ake Kira Namijin Dare

Aljanin Da Ake Kira Namijin Dare

by
3 years ago
0

...

Abubuwan Da ke Kawo Toshewar Hanyoyin Jini

by
3 years ago
0

...

Next Post

Yawan Karanta Littattafan Hausa Ya Sa Ni Sha’awar Rubuta Littafi — Rahmatu

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: