Yayin da Nijeriya take bikin murnar cika fiye da shekara ashirin da kasancewa cikin mulkin dimokuradiyya bai samu wata tangarda ba tun shekarar 1999.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shi ya bayyana hakan a jawabinsa na bakin ranar dimokuradiyya, ya yi kira da ‘yan Nijeriya su kara hakuri domin kuwa gwamnatisa za ta yi duk mai yuwuwa wajen saukaka matsalar rayuwar bayan cire tallafin mai.
- Da Dumi-dumi: Dakataccen Shugaban EFCC, Bawa Ya Shiga Hannun DSS
- Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Bawa Har Illa-masha Allah
Wannan ta kasance ne kamar jirwaye mai kamar wanka saboda kuwa ana ta yi mata kiraye-kiraye na ta kyautatawa rayuwar al’umma. Irin wadannan kiraye- kirayen na tafiyar da gwamnati kamar yadda ya dace ya fito ne wurin kungiyar NADECO da ta yi kira da Tinubu da ya aiwatar da rahoton shawarar da Mallam Nasir el-Rufai ya yi kan cika manufofin jam’iyyar APC na maida Nijeriya ga tsarin gwmnatin tarayya.
 Sai dai kuma jawabin da shugaban kasa ya yi wa ‘yan Nijeriya ta kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin, ya kara tunatar da ‘yan Nijeriya kan niyyar da yake da shi ta sauwaka masu irin halin da suke ciki na tsadar rayuwa.
Ya yi alkawari zuba jari a bangaren zirga-zirgan da abubuwan more rayuwa kamar ilmi, wutar lantarki, kula da lafiyar al’umma da sauran abubuwa domin bunkasawa da kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ya yi bayani kan muhimmancin ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar mai cike da tarihi ga Nijeriya kamar dai yadda ya yi kira da ‘yan Nijeriya su kare mulkin dimokuradiyya wadda kafin ta kafu an sha gwagwagwa.
Tinubu ya yi jinjina da tunawa da Marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola da sauran masu kishin kasa da suka rasa rayuwarsu saboda fafutukar tsayuwar dimokuradiyya a Nijeriya.
 Da yake danganta ayyukan da gwamnati ya kamata ta yi da maganar cire tallafin man fetur kuwa, shugaban kasa ya bayyana dalilin da ya sa aka cire tallafin man fetur domin ya san irin wahalar da ‘yan Nijeriya suke sha. Ya ce hakurin da suka yi na jure wahalar da ake sha ba zai tafi a banza ba.