Sarkin Fulanin Jihar Edo, Alhaji Muhammadu Sosal ya yi kira ga gwamnatin jihar Edo da ta yi wa Allah da Annabinsa ta janye dokar da tasa na korar Fulani a jihar baki daya.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan hukuncin kwana 5 da kwamnatin ta ba kowani bafulatani ya bar jihar.
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
- Harin Jirgin Kasa: Mutane 7 Sun Samu ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga Bayan Gumi Ya Shiga Tsakani
Sarkin ya ce a gaskiya daukar wannan mataki zai cutar da fulanin da ke zaune a dukkan fadin jihar bisa ga yadda mafi yawan fulanin da ke zaune a jihar sun haura shekaru 30 zuwa 50 a jihar ba tare da an same su da wani laifi ba.
Basaraken ya ce mai zai hana a gaya masu laifin da suka yi kafin a kore su.
Sannan ya tabbatar da cewa su ba sa mara wa duk wani batakarin fulani baya, kuma ba su yadda da ta’addanci ba kuma suna goyan bayan hukunta duk wanda ya yi laifi.
Tuni sarkin ya janyo hankalin gwamnati da ta ba su damar saurarensu mai makon ba su kwana biyar musamman a irin wannan yanayin.
Shugaban ya ce “Ina da tabbacin duk inda muka je babu wanda zai yarda da mu saboda yanayin da ake ciki na rashin aminci.”
Don haka yana son a sauraresu don su ji dalilin korar tasu bayan da yawan fulani suna da gonaki da suka yi shuka kuma amfani ya yi girma sosai.
Ya kara da cewa Jihar Edo jiharsu ce tun da da yawansu a nan aka haife su. Bisa haka sarkin ya yi kira ga gwamna da duk sauran masu fada a ji su sa baki don gyara lamarin domin a cewarsa ba dukkan fulani suka zama lalatattu ba, akwai masu tsoran Allah da kiyaye doka.
Ya e yanzu haka suna da labarin an fara kona musu gidaje a wasu yankin jihar, bisa haka sarkin ya nemi gwamnati ta duba wannan lamarin don daukar mataki.