Khalid Idris Doya" />

Korona: An Sallami Fursunoni 175 A Gombe

A kokarin gwamnatin Gombe na rage cinkoson Fursunoni musamman a irin wannan lokacin da ake fama da cutar Korona, gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya yayi afuwa ga Fursunoni guda 60 da suke gidajen gyara halinka daban-daban a fadin jihar.

Idan kuma aka sallami Fursunoni guda 115 daga gidajen yarin ta hanyar beli domin rage cinkoso da cakuduwa a gidajen yarin da suke jihar.

Kwamishinan shari’a na jihar Zubair M. Umar shine ya sanar da hakan a cikin kwafin sanarwar manema labaru da ya fitar a jiya, yana mai cewa, gidajen yari da suke jihar da dama ana fuskantar cinkoso wanda gidajen yarin ke dauke da Fursunoni fiye da adadin da aka gina gidajen da zummar zaunar da Fursunonin a cikinsu, wanda ya ce akwai gayar bukatar shawo kan matsalar.

A cewar kwamishinan, “A ranar 26 ga watan Maris, 2020 mun bukaci Kwantirolan gidan gyara halinka na jihar da ya zo da tsarin da zai kai ga hada kai da ma’aikatar shari’a da bangaren shari’a na jihar domin ganin hanyoyin da za a bi na rage cinkoso a gidan yarin.

“A ranar 30 ga watan Maris, 2020 Kwantirolar ya gabatar da jerin sunayen Fursunoni 300 domin a yi la’akari da su. Bayan fito da jerin sunayen wadanda ake zargi da laifukan da suka hada da fyade da laifukan ta da hankali, mun roki mai rikon Babban Jojin jihar da ya umurci Alkalai da su yi tayin beli wa Fursunoni 174. Bayan kammala wannan aikin, Fursunoni 115 an sakesu ta hanyar beli daga gidajen yarin, inda a yanzu haka ana ci gaba da kokarin ganin belin Fursunoni 59 ya samu kammaluwa.”

Kwamishinan shari’a na jihar Zubair M. Umar ya kara da cewa, “Wakazalika, a ranar 6 ga watan Afrilun 2020, mun sake bukatar Kwantirola na gidan yari da ya rubuta bukatar bada shawara ga majalisar bada shawarar yin afuwa wa Fursunoni domin ganin an sake wadanda suka cancanci gwamnan jihar ya musu afuwa.

“Majalisar bada shawara kan afuwar ya amshi bukatar sake Fursunoni 29 da ake rokon gwamnan da ya musu afuwa bisa laifukansu daban-daban da ake fuskanta a kotuna daban-daban.

“Majalisar afuwar ya tantance tare da bada shawara wa gwamnan da yayi afuwa ga Fursunoni 28. Su wadannan Fursunonin kotuna daban-daban a Gombe sun samesu da aikata laifuka tare da yanke musu hukunci da suke zaman wakafi a gidan yarin gyara halin da ke Gombe da na Bajoga da Billiri, Cham gami da kuma gidan yarin Tula.”

A cewar kwamishinan nan take bayan musu afuwar aka sakesu daga gidajen yarin tare da maidasu kananan hukumominsu.

Ya kara da cewa, “Idan za ku iya tunawa a ranar 9 ga watan Fabrairu, 2020 gwamnan Gombe yayi afuwa wa Fursunoni 32 da suke gidajen gyara halinka daban-daban. Dukkanin adadin wadanda aka sake kawo yanzu Fursunoni dari da saba’in da biyar (175).” A cewar Kwamishinan shari’a na jihar Zubair M. Umar.

Exit mobile version