Bauchi, " />

Korona: BASIEC Ta Dage Zaben Shugabannin Kananan Hukumomin Bauchi

Hukumar shirya zabuka ta jihar Bauchi (BASIEC) ta dage da yin zaben shugabannin kananan hukumomin jihar a sakamakon annobar cutar Koronabairus.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da hukumar ta ranar a Bauchi jiya, dauke da sanya hannun shugaban hukumar shirya zabuka na jihar, Dahiru Tata, ya shaida cewa daukar matakin hakan na zuwa bayan da cutar Koronabairus ta zama babban annoba ga kasashen duniya.

Wakilinmu ya nakalto cewar a kwanakin baya dai Hukumar dai ta fitar da sanarwa ta cikin wasika mai kanu kamar haka BA/SIEC/OFF/175 mai dauke da kwanan wata 17 ga watan Maris da suka sanar da cewar za su gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin jihar a ranar Asabar ga watan June na shekarar 2020.

Takardar manema labarum da hukumar ta rabar a jiya ta shaida cewar dakatar da gudanar da zaben na da nasaba da annobar cutar Korona da ta addabi duniya, “Muna farin cikin sanar muku cewar a bisa annoba cutar Koronabairus da ta addabi duniya. Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ya amince da dakatar da zaben shugabannin kananan hukumomi da aka tsara gudanarwa a watan June 2020 nan da nan,” A cewar sanarwar.

Sai dai sanarwar ba ta kuma sanar da sabon lokacin da za a gudanar da zaben ba, illa dai an dage zaben sakamakon kunnowan kan cutar Corona.

Jihar Bauchi dai na da mutum uku da suka kamu da cutar ciki kuwa har da gwamnan jihar Bala Muhammad da kansa tare da abokinsa na kut da kut da wani na kusa da shi.

Kawo yanzu dai jihar ta sha alwashin yaki da cutar tare da hana shiga da fita a kokarinta na yaki da cutar ta Korona, inda ma wakilinmu ya nakalto mana cewar dokar rufe jihar kirif tare da haramta shiga da fice a jihar zai fara aiki ne daga karfe shida na yammacin yau Alhamis.

Exit mobile version