Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad Abdulkadir ya yaba wa gidauniyar BUA bisa ayyukan tallafi da take yi wa gwamnatoci da hukumomin gwamnatocin jihohi da ta tarayya dangane da yaki da cutar sarkewar numfashi (Korona).
Kamfanin BUA dai ya baiwa jihar Bauchi tallafin Motocin daukan marasa lafiya (ambulas) har guda uku sabbi tare da takunkumin rufe hanci da baki na kariya daga Korona guda dubu dari biyar domin tallafa wa kokarin gwamnatin jihar kan yaki da cutar Korona.
Gwamnan ya yi wannan yabo ne ranar Litinin lokacin da ya ke karbar tallafi daga rukunonin kamfanin BUA da Gidauniyarta a madadin gwamnati da daukacin jama’ar jihar Bauchi, inda ya ke cewar, “Ina bayyana farin cikina ga shugaban rukunin kamfanonin BUA saboda wannan aiki na jin kai da ta yi wa mutanen jihar mu ta Bauchi,”
Sanata Bala Mohammed ya bayyana shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul’samad Ishiyaka Rabi’u da cewar shi fitaccen mai jin kai ne, kuma mashahurin dan-kasuwa wanda ya kamata a rika koyi da shi.
Da ya ke jawabi a kusa da shugaban kwamitin yaki da cutar Korona a jihar kuma mataimakin gwamnan jihar Sanata Baba Tela, gwamnan ya kuma gode wa Shugaban gidauniyar BUA da abokan tafiyarta na gama kai kan cutar Korona bisa tallafin rage radadin da suka baiwa ‘yan Nijeriya.
Bala, ya bayyana rukunin kamfanin BUA da cewar gidan kowa a kwai kayayyakin da da suke samarwa a Nijeriya da suka hada da siminti da albarkatun gona, yana mai cewar jihar Bauchi tana tutiya da irin wadannan kayyyakin.
Nan take gwamnan ya mika kayayyakin ga Shugaban Kwamitin karta-kwana kan yaki da cutar Korona Baba Tela domin tafiyar da su yadda ya dace.
Tun da farko da ya ke mika tallafin ga gwamnan, tsohon Ministan lafiya, Dakta Adi Ali Hong, ya shaida cewa, “Ina wakiltar Shugaban rukunin kamfanin BUA kuma shugaba ga gidauniyar Alhaji Abdulsamad Ishiyaka Rabi’u a wannan bikin mai kayatarwa.”
Ya kuma yaba wa kokarin gwamnatin jihar kan yaki da cutar Korona, yana mai cewar, yanzu haka duniya tana sake fuskartar zagaye na biyu na Cutar Korona, wanda tuni cutar ta sake bayyana a kasar Amurka da Turai, har ma da Najeriya kamar yadda yaduwar cutar ke kara bayyana a wurare dabam-dabam.
Dr. Idi Hong ya bayyana cewar, gidauniyar BUA ya yi tallafin Jin kai na misalin naira Biliyan takwas a fadin kasar nan wa gwamnatocin jihohi da na tarayya da hukumomin su ta hanyar kayayyakin da kamfanoni su ke sarrafawa da suka hada da kayayyakin abinci da kayan gine-gine.
Alhaji Abdul’samad Ishiyaka Rabi’u ya kuma bayar da tabbacin cigaba da ayyukan tallafi ta yadda za a kori cutar daga kasar nan.