Korona: Gwamnati Ta Nemi Saudiyya Ta Dage Takunkumi Kan ‘Yan Nijeriya

Gwamnatin tarayya ta bukaci kasar Saudiyya da ta dage takunkumin hana zirga-zirgar da ta sanya wa matafiya ‘yan Nijeriya biyo bayan bullar cutar Omicron a kasar Afirka ta Kudu da aka gano a tsakanin wasu matafiya da aka ce sun ziyarci Nijeriya.

Ambasada Zubairu Dada, Karamin Ministan Harkokin Waje ne ya yi wannan roko a ranar Asabar lokacin da ya gana da Jakadan Saudiyya a Nijeriya Ambasada Faisal bin Ebraheem Al-Ghamdi.

Dada a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Ibrahim Aliyu ya fitar, ya bukaci mahukuntan Saudiyya da su sake duba takunkumin hana zirga-zirgar da suka sanya wa ‘yan Nijeriya dangane da bullar cutar Omicron kamar yadda kasashe da dama da suka haramtawa Nijeriya shiga kasarsu tun da farko suka koma suka yi nazarin nasarorin da Nijeriya ta samu game da yaki da cutar da takwararta Korona, sannan suka dage haramcin.

Exit mobile version