A ci gaba da kokarin da ake yi na tunkarar cutar korona, rundunar Sojojin sama ta Nijeriya (NAF) a ranar 3 ga Disamba, 2020, ta kaddamar da wani shirin horaswa na kwanaki 2 ga masana kimiyyar dakin binciken gwaje-gwaje kan amfani da injin ‘GeneDpert’ na gwajin cutar korona.
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, da yake jawabi yayin bikin, Babban Hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, wanda ya samu wakilcin Babban Hafsan a fannin jiragen sama na ‘Tactical Air Command’ (TAC), Air Commodore, Shehu Bakari, ya bayyana cewa, Kimiyyar ‘Laboratory Medical’ a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan na kowane tsarin kiwon lafiya, inda ya kara da cewa, NAF ta yi matukar saka jari ta fuskar sayen kayan aikin likitanci na zamani, inganta kayayyakin more rayuwa tare da inganta karfin masana kimiyyar dakin binciken ta.
Ya ci gaba da cewa, saboda barkewar annobar korona, NAF ta ga ya dace ta sayi kayan aiki na musamman don gwajin cutar. Wannan, in ji shi, an yi shi ne don baiwa ma’aikatan NAF damar bunkasa kwarewar da ake bukata domin bunkasa karfin gwajin su, musamman a aikin injinan ‘GeneDpert’, wanda za a tura zuwa Asibitocin NAF a duk fadin kasar.
A cewarsa, wannan shirin zai taimaka wajen dakile yaduwar korona a cikin kasa. Ya kuma sake nanata cewa, za kuma a iya amfani da injin ‘GeneDpert’ wajen gano wasu kwayoyin cuta kamar ‘Tuberculosis’, ‘Hepatitis B’ da C da tarin fuka, ma’ana ‘Flu birus’.
Shi ma da yake magana a wajen taron, Shugaban kula da lafiya na hedikwatar NAF, Air Commodore, Gideon Bako, ya bayyana cewa, babu shakka bitar zata kara bunkasa kwarewar masana kimiyyar dakin gwaje-gwajen wajen yin gwajin korona. Ya kuma nuna kwarin gwiwarsa cewa, tura injinan GeneDpert a wasu cibiyoyin lafiya na NAF zai taimaka kwarai da gaske wajen cimma burin da aka sa gaba na ganowa cikin sauri, warewa da kuma kula da masu cutar korona. Don haka ya umarci mahalarta taron da su yi amfani sosai da horon da aka basu kuma su tabbatar da cewa ilimin da aka samu ya fassara zuwa ingantattun ayyukan ddakin gwaje-gwaje a cibiyoyin kiwon lafiyar su.