Dangane da karuwar masu kamuwa da cutar Korona a duk fadin kasar, Babban Hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar ne ya umurci Shugabannin sojojin saman Nijeriya (NAF) na bangaren mahadar Iskar Shaka ‘Likuid Odygen (LOD)’ a rukunin ‘103 Strike Group (103 STG)’, Yola, don habaka aikin samar da iskar shaka ‘LOD’ don rarrabawa zuwa cibiyoyin kula da cutar.
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Bice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, a bin wannan umarnin ne, hukumar a ranar 16 ga Disamba 2020, ta rarraba silinda 117 na LOD zuwa cibiyoyi biyu na kula da cutar a Abuja.
Cibiyoyin da suka ci gajiyar su ne Asibitin Koyarwa na jami’ar Abuja, Gwawalada, da cibiyar kiwon Lafiya ta DSS, Asokoro.
A ranar 10 ga Yulin 2017, mahadar 103 STG LOD Yola, na da karfin samar da lita 1,000 na LOD kowane awa 8, wanda ya ma wuce abin da NAF ke bukata don ayyukanta na sama da kuma amfani da su a cibiyoyin Kiwon Lafiya na cikin kasar.
Shugaban ya ba da tabbacin cewa NAF za ta ci gaba da samar da da iskar LOD kyauta, baya ga ayyukan jigilar sama, a ci gaba da goyon bayan kokarin da gwamnati ke yi na yakar cutar ta korona a duk fadin kasar.