Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: PHCDA Ta Horar Da Jami’an Kiwon Lafiya 5,000

Published

on

Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko (PHCDA) ta horar da jami’an kiwon lafiya sama da dubu biyar da kungiyoyi masu zaman kansu kan yadda zasu taimaka wajen yaki da annobar Koronabiarus.

Babban daraktan hukumar, Dakta Ibrahim Ahmed Dangana ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishin shi da ke Minna. Yace ganin yadda gwamnatin jiha ta himmantu wajen yaki da annobar Korona, ganin yankunan karkaru na bukatar kulawa, hukumar ta samar da dukkanin kayan kariya ga jami’an kiwon lafiya a dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar ga cibiyoyin kiwon lafiyar da ke yankunan karkara domin ba su damar kulawa da yin aiki yadda ya dace.
Yanzu haka bayan maganar Korona akwai wasu yankunan kananan hukumomi da ke fuskantar barazanar mahara, wanda ko a cikin kwanakin jami’in daya ya rasa ransa a karamar hukumar Munya, hakan bai kashe mana guiwa ba, za mu cigaba da sauke nauyin da ke kan mu na kulawa da lafiyar al’ummar mu bisa tsare tsaren ma’aikatar lafiya ta jiha.
Dakta Dangana, yace idan muka duba muna fuskantar matsaloli da dama musamman canjin yanayi, wanda sare itatuwa ban cin barnar da yake haddasawa na lalata kasa yana tasiri wajen gurbata yanayi, da ke shafar lafiyar jama’a. Maganar gaskiya yanke itatuwa na kawo Wa yanayi illa, wanda ya kamata duk inda aka sare itace a tabbatar an sake shuka wani.
Dakta Dangana yace kusan dukkanin matsalolin da ke tasowa daga annobar Korona, hare hare ‘yan bindiga da canjin yanayi hukumarsa na daukar matakan da suka dace dan ganin al’umma suna samun kulawar ma’aikatar kiwon lafiya har a yankunan karkarun jihar.
Yanzu haka gwamnatin jiha ta kafa kwamitin kula da annobar Korona a jiha wadda ke aiki ba dare ba rana sannan duk wani shawarar da hukumar lafiya ke bayarwa wannan kwamitin tana aiki da shi yadda ya kamata, mu kuma a bangaren kiwon lafiya duk wasu matakan da ya kamata mu dauka muna daukarsa yadda ya kamata domin muna samun hadin kan gwamnatin da duk wani abu da muke bukata.
Saboda haka duk wani matakin da ake bukata a bangaren kiwon lafiya ta yadda al’ummar karkara zasu anfani gwamnati muna yinsa, shi yasa komai zaman karkara da nisan sa da duk wani hadarin da ake fuskanta na tsaro da wani abun jami’an mu suna wajen shi yasa gwamnati ta samu kwarin guiwar cigaba da inganta kananan asibitoci ta fuskar kayan aiki da ma’aikata, mun dauki matakai da dama musamman wajen horar da jami’an kiwon lafiya da ba su kwarin guiwar yadda za su gudanar da aiki yadda ya kamata.
Ba mu yi sanyin guiwa ba, mun dauki matakan da suka da ce wajen horar da jami’an mu, da kungiyoyin sa ka da kuma shugabannin al’umma domin wayar da kan mutanen karkara wanda haka ne yasa muke samun nasara a bangaren kiwon lafiya, saboda haka ba za mu gajiya ba wajen cigaba da baiwa kiwon lafiya muhimmanci domin anfanin jama’ar jihar nan.
Ina kira ga al’umma musamman mutanen karkara da cewar annobar Korona gaskiya ce, ya kamata duk wani shawarwarin da hukumomi lafiya ke bayarwa su kiyaye shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: