Connect with us

RAHOTANNI

Korona: Sanya Dokar Hana Zirgz-zirgz Ya Yi Dai-dai Ga Wasu Magidanta—-Hauwa Inuwa.

Published

on

Sanya dokar zaman gida dole a jihar Gombe sakamakon bullar cutar Korona birus ta yi was Mata Irina dai dai saboda rashin mutunta mata da wasu Mazaje keyi na rashin sauke hakkoin dake kansu yadda Allah ya wajabta musu.
Hajiya Hauwa Muhammed Inuwa Gombe ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da Leadership a Yau Lahadi sakamakon sanya dokar shiga gida da gwamnatin jihar Gombe tayi daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 7 na safiya.
Hajiya Hauwa Muhammed tace a baya kafin wannan dokar wasu mazaje basa mutunta Matan su basu da lokacin su balle ma su dawo gida akan lokaci Iyalan su su gansu har su san damuwar matan nasu amma yanzu dole ta sa Mazaje na komawa gida akan lokaci.
Ta kuma kara da cewa sai dai irin matan da suke murna da wannan dokar ta zaman gida matan da mazajen su suke da wadata ne basa dawo wa gida su sami lokacin iyalan su amma yanzu wannan dokar ta sa su dole su dinga dawowa gida.
Har ila yau ta kara da cewa irin wadannan mazaje idan suka dawo gidan ma maimakon su zauna da iyalansu suji damuwowin su sai kaga suna ta hira da wasu mata daban a waya bayan ga Matar sa a gefen sa ya rabu da ita.
Hauwa ta kuma ce matan da Mazajen su kuma basu da wadata idan Mace tayi murna ma ya zama banza saboda idan Mijin ya dawo gida ya zauna me za su ci a lokacin da aka nemi abu aka rasa ita za ta fara cewa mijin ya fita yasan yadda zai yi dasu.
A cewar ta dokar tana da alheri ta wani waje kuma bata dashi domin cutar tazowa mutane a lokacin da jama’a dake fama da matsalar rayuwa.
Sannan Hauwa Muhammad Inuwa, ta shawarci jama’a da su yi wa gwamnati da’a da biyayya dan a samu saukin shawo kan wannan cutar.
Daga na sai ta yi kira ga gwamnati da cewa tunda an sanya dokar zaman gida a duk lokacin da aka shiga gida ta samar da wani lokaci ana feshin Magani a wurare daban daban dan ganin an yaki wannan cutar ta korona.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: