A sakamakon umurnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na dakatar da wasu fasinjoji 100 daga balaguro zuwa kasashen waje saboda kin bin dokar gwajin Korona na kwana bakwai ga daukacin masu tafiye-tafiyen waje, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya umurci sassan hukumar da suka dace su tabbatar da cika umurnin gwamnati
Umurnin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar ya fitar a yau Litinin ta hannun Jami’in hulda da jama’a na hukumar, DCI Sunday James.
Sanarwar ta kara da cewa, fasinjojin da suka yi laifin, an dakatar da su daga tafiye-tafiye na tsawon wata shida, “daga 1 ga Janairu 2021 zuwa 30 ga Yunin 2021. An riga an sanar da dukkan fasinjojin da abin ya shafa kuma za a hana su sake sabunta fasfo da duk wata balaguro zuwa waje a tsakanin wannan lokacin,” in ji sanarwar.
Hukumar shige da ficen ta kuma gargadi dukkan fasinjojin da abin ya shafa su bi umurnin domin kauce wa jefa kiwon lafiyar al’umma cikin hadari.