Wata kotun majistare da ke Jihar Ogun, ta bayar da belin shahararren mawaki Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, bayan gurfanar da shi a gabanta a yau Litinin.
Rundunar ‘yan sandan jihar, ce ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da farmakar wasu ‘yan sanda da ke bakin aiki.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta tuhumar da aka karanta masa.
Lokacin da ya yanke shari’a, alkalin kotun, A.S Shoneye ya ce za a iya bayar da belin wanda ake tuhuma da irin wanna laifi.
A kan haka ne ya bayar da belin nasa kan kudi N300,000 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.
Sai dai kotun ta bayar da umarnin tsare Portable a gidan gyaran hali har sai ya cika ka’idojin belin.
Yanzu haka kotun ta dage sauraren karar har sai ranar 26 ga watan Afrilu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp