Wata kotu da ke yankin Lugbe a Abuja ta yanke wa Terkaa Akishi mai shekaru 36 hukuncin daurin watanni 15 a gidan gyaran hali saboda satar Alkur’ani mai girma.
Alkalin kotun, Malam Aliyu Kagarko ya daure barawon ne bayan ya amsa laifinsa a gaban kotu.
- An Fara Taron Kasa Da Kasa Kan Tsarin Dimokuradiyya Karo Na Uku A Nan Birnin Beijing
- Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2
Rundunar ’yansandan Abuja ce ta gurfanar Terkaa bayan ya saci wayar salula da Alkur’ani guda biyu a wani Masallacin da ke barikin sojojin a unguwar Asokoro.
Mai gabatar da kara, Emeka Ezeganya ya ce, laifin da Terkaa ya aikata na keta haddi da kuma sata ya ci karo da sashe na 348 da kuma na 287 a kundin final kod.
Mista Ezeganya, ya ce wata mai suna Balikisu Isah da ke barikin sojin a Asokoro ce ta kai kara wurin ‘yansandan yankin.
Bayan gudanar da bincike ne ‘yansanda suka mika shi ga kotu domin a hukunta shi daidai da laifinsa.
Alkalin ya bai wa Terkaa zabin biyan tara ta Naira 40,000 ko kuma zaman kaso na watanni 15, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Nijeriya (NAN), ya bayyana.