Lokacin da Karen ta farka daga bacci a wani asibitin El Salbador, ta lura cewa an saka mata ankwa a hannu sannan kuma ga ‘yan sanda a gefenta.
“Akwai mutane da yawa a wurin kuma suna ta cewa wai na kashe jaririna kuma ‘sai na fuskanci hukuncin abin da na aikata’,” kamar yadda Karen ta shaida wa BBC.
Tana bukatar kulawar gaggawa saboda wahalar zubewar ciki. Amma Karen, mai shekara 22 a lokacin, ta tsinci kanta cikin zargin zubar da ciki.
“Na yi yunkurin yin bayanin abin da ya faru, amma suka ki sauraro na,” a cewarta.
Tsattsaurar Doka
El Salbador, da ke nahiyar Tsakiyar Amurka, na daya daga cikin kasashen da suka fi tsaurin doka kan zubar da ciki, wadda ta haramta duk wani nau’i na zubar da shi, ko da kuwa na barazana ga rayuwar mace ko an yi shi ta hanyar fyade ko kuma ‘yan uwa ne suka yi shi.
Karen, wadda aka tuhuma da kisan kai, an yanke mata hukuncin daurin shekara 30 a gida yari. Tana cikin rukunin mutanen da aka kira “Las 17”, wadanda aka taba yanke wa hukuncin dauri saboda yin bari ko kuma haihuwar jariri babu rai.
Karen ta shafe shekara shida a garkame kafin daga baya a sako ta tare da wasu mata uku a watan Disamban 2021 sakamakon wani matsin lamba daga kasashen duniya.
A lokacin da aka tsare ta, Karen na da da mai shekara biyu. Karen ba ta sake ganin sa ba har sai da ya kai shekara tara.
‘Na so na rungume marigayin dana a hannayena’
Daya daga cikinsu ita ce Cinthya, wadda aka daure a 2009 kan kisan kai bayan danta ya mutu saboda an haife shi bakwaini. An sake ta a 2019.
Cinthya ta fada wa BBC cewa maimakon a nema mata motar daukar marasa lafiya, ‘yan sanda ne suka isa wurin. Ta sume, kuma ko da ta farka a asibiti, kamar Karen, sai kawai ta ga ankwa a hannunta.
An tafi da ita daga asibiti zuwa ofishin ‘yan sanda kai-tsaye kafin a fara yi mata shari’a. Ba a ba ta damar gani ko yin magana da ‘yan uwanta ba, hasali ma ko gawar dan nata ba ta gani ba. Shekararta 20 a lokacin.
“Na so na rungumi dana a hannuna, amma ba a ba ni dama ba. Haka ma ba su bar ni na je jana’izarsa ba,” in ji Cbthya.
Karen ta ce ta fuskanci irin wannan matsalar a kotu amma ta yi a cikin bursin saboda ta samu kanta cikin sauran matan da aka daure su bisa tuhumar zubar da ciki.
“Mu kusan 10 ne kuma wasu daga cikin matan sun fuskanci cin zarafi daga wasu fursunonin,” a cewarta.
“Daga baya sai muka kafa wata kungiya don taimaka wa junanmu.” Tasiri mara dadi.
Ba abu ne mai yiwuwa ba a iya cewa dukkanin cikin da suka zube ba matan ne suka zubar da su ba, amma masu fafutika na cewa dokokin na yanzu na daure matan da ba su zubar da cikin da gangan ba.
Masu kare hakkin mata a El Salbador na cewa lamarin ya fi shafar matan da ba su da arziki sosai da za su iya samun kulawa daga asibitoci masu zaman kansu.
Mata kamar Cinthya da Karen.
“Mata matalauta ne suka fuskantar matsala da irin wadannan dokoki da ke jawo musu tsana kuma suke sa wasu su aikata zubar da cikin,” in ji Morena Herrera, wata shahararriyar mai fafutika a El Salbador.
Cinthya ta yi ikirarin cewa lokacin da ake yi mata shari’a ba a bari ta yi magana ba a kotu. Haka nan, ba a bari an kai mata ziyara ba ko kuma yi mata bayani daga lauyan da gwamnati ta ba ta lokacin da take jiran shari’a a gidan yari. Ba ta ma san tuhumar da ake yi mata ba takamaimai. “Har sai a kotu sannan na ji cewa ana tuhuma ta da kisan kai,” a cewarta.
BBC ta nemi mahukuntan EL Salbador su mayar da martani game da zarge-zargen amma ba mu samu amsa ba. A cewar alkaluman wata cibiya da ke Amurka mai suna Center for Reproduction Rights, El Salbador na cikin kasashe bakawai a Tsakiyar Amurka da suka haramta zubar da ciki kwatakwata.
Honduras, da Jamaica, da Nicaragua, da Haiti, da Dominican Republican, da kuma Surinam ne sauran kasashen (a fadin duniya kuma, kasashen da suka haramta zubar da ciki kwatakwata 24 ne).
‘Wani kulli ne da ba shi da alamar warwarewa’
Har yanzu akan daure matan da suka yi bari a El Salbador. A watan da ya gabata ma an daure wata mace da aka bayyana da “Esme” shekara 30 a gidan yari. “Har ila yau ana daure mata irina a gidan yari. Wani kulli ne da ba shi da alamar warwarewa,” a cewar Cinthya.
Bayan an sako ta, Cinthya ta sha wahala wajen neman aikin yi saboda tarihin laifinta, amma sakamakon wani taimako da ta samu daga wata kungiya ta samu damar gudanar da harkokin sayar da tufafi.
Ta haifi wata yarinya a 2020 mai suna Marcela Elizabeth. “Na firgita lokacin da na samu ciki, saboda tsoron zan sake fadawa cikin abin nan idan aka samu matsala,” a cewar Cinthya.
“Amma an haife ta kalau ba tare da wata matsala ba. Ita ce farin cikina.”
Karen ta ce tana jin cewa mutane na nuna mata yatsa amma yanzu ta mayar da hankali kan karatun sakandare da ta fara a gidan yari da kuma sake kulla alaka da danta. Karen na ganin bayar da labarinta zai taimaka wa wasu matan.
“Har yanzu akwai abubuwan da ke damu na da ba zan manta da su ba. Amma magana a kansu za su iya taimakawa wajen dakile faruwar wasu abubuwan kuma ya taimaka wa wasu kawayena da har yanzu suke a daure.” Mun samu wannan rahoto daga BBC.