Alkalin babbar kotun shari’a Musulunci da ke Jihar Kano, mai shari’a Abdullahi Halliru, ya yi watsi da bukatar da lauyan da ke kare Inuwa Uba mijin.
Asiya, ‘yar cikin gwamnan Kano, Abudullahi Umar Ganduje, na kalubantar da lauyan cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar.
- Rikicin Warware Rawanin Tsohon Wazirin Bauchi Na Ci Gaba Da Daukar Sabon Salo
- Asalin Abin Da Ya Faru Tsakanin Abba Gida-gida Da Uwargidan Shugaban DSS
Asiya ta shigar da karar ne, ta hanyar lauyanta Barista Ibrahim Nassarawa, inda ta bukaci kotun da ta raba aurenta da Inuwa ta hanyar Khul’i.
Asiya dai, a cikin bukatar da ta bai wa kotun, ta ce, a shirye take ta biya Inuwa sadakin auren da ya ba ta Naira 50,000.
A yayin da kotun ta dawo sake sauraren karar a zaman da ta yi a ranar Alhamis domin yanke hukunci a kan takadar karar ta Asiya, alkalin kotun, ya bayyana cewa, kotunsa na da hurumin sauraren karar.
Alkalin ya kuma tambayi lauyan wanda ake karar cewar, ko ya san nawa ne Inuwa ya biya a matsayin sadakin Asiya lokacin da aka daura auren, inda lauyan ya shaida wa alkalin cewar ba shi da masaniya.
Lauyan wanda ake karar da kuma wanda ke tsayawa, sun bukaci kotun ta dan tsahirta musu don su Asiya da mijin nata Inuwa don sanin nawa ne adadin sadakin, inda kotun ta amsa bukatar tasu.
Kowanensu ya fita daga cikin dakin kotun don buga wayar tafi da gidanka ga wadanda suke karewa a gaban kotu.
Bayan da kotun ta dawo daga gajeren hutu, lauyan wanda ake karar ya shaida wa kotun cewa, bai samu wanda yake karewa a waya ba, inda ya bukaci kotun ta dage sauraren karar don ya samu ya ji daga bakin wanda ya ke karewa kan nawa ya biya sadakin.
A nasa bangaren lauyan da ke tsayawa mai karar ya hakikance cewa, Inuwa ya bai wa Asiya Naira 50,000 a matsayin sadakin aurenta, inda ya ce, Asiya ta ce, a shirye take ta biya Inuwa Naira 50,000 don a raba auren nasu.
Bayan kammala sauraren duk bangarorin biyu, alkalin kotun ya dage sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Janairu 2023, domin lauyan wanda ake karar ya samu shaidawa kotun adadin sadakin auren da Inuwa ya bai wa Asiya kafin alkalin ya shiga mataki na gaba a kan shari’ar.