Babbar kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin hana hukumomin tarayya kawowa kudaden da ake warewa kananan hukumomi 44 na Jihar Kano tsaiko.Â
Wannan umarni ya biyo bayan karar da wasu ma’aikatan kananan hukumomi da sauran mazauna jihar suka shigar, suna fargabar cewa kudaden na iya samun jinkiri ko kuma a hana su gaba daya.
- Real Madrid: Me Ke Faruwa Ne A Santiago?
- Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Atamfar HaÉ—in Kan Ƙasa Da Tallafin Littafi 50,000 A ZamfaraÂ
Mai Shari’a Ibrahim Musa Muhammad, wanda ya bayar da wannan umarni, ya bai wa masu shigar da kara damar aikewa da takardun kotu zuwa Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Babban Bankin Nijeriya (CBN), da Hukumar Rarraba Kudade da Albarkatun Gwamnati (RMAFC).
Kotun ta nada kamfanin Red Star Express don taimakawa wajen kai takardun, kasancewar hukumomin suna wajen yankin kotun Kano.
Umarni na wucin gadi na kotun ya hana hukumomin tarayya tsoma baki ko tsaida kudaden kananan hukumomin har zuwa lokacin da za a sake sauraron karar a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2024.
Mai Shari’a Muhammad ya jaddada cewa kada hukumomin su dauki wani mataki da zai hana ko rage kudaden a wannan lokacin.