Wata babbar kotu a Kano ta bayar da umarnin hana hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) kama Sanata Rabi’u Kwankwaso da wasu mutane shida.
Alkalin kotun mai shari’a Yusuf Ubale Muhammad ne ya bayar da wannan umarni, inda ya haramtawa hukumar EFCC kamawa, da tursasa, da tsarewa, da kuma tsoratarwa, har sai an saurari ƙarar da kuma tantance buƙatar da aka shigar a ranar 5 ga watan Yuni 2024. Wannan hukuncin ya zo ne a yayin da ake ci gaba da bincike.
EFCC na zargin karkatar da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe da suka kai Naira biliyan ₦2.5b da tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya yi.
Umurnin wucin gadi na Mai shari’a Muhammad ya tabbatar da cewa hukumar EFCC, da jami’anta, da duk wani bangare da ke da alaka da su an hana su cin zarafin masu ƙara.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin a mika wa EFCC umarnin na wucin gadi tare da bukatar da aka gabatar a kan sanarwa da duk wasu takardun da suka dace a mika su ga hukumar ta EFCC nan take kafin ranar da za a dawo kotu.
A ranar 24 ga watan Yunin 2024 ne za a ci gaba da sauraren shari’ar a kan ƙudirin da aka gabatar, wanda zai ƙara tantance shari’ar da hukumar EFCC ta yi wa Kwankwaso da sauran mutanen da abin ya shafa.
Sakamakon zaman da za a yi a ranar 24 ga watan Yuni zai kasance muhimmi wajen tantance ko EFCC za ta iya ci gaba da gudanar da ayyukanta ko kuma dokar hana kama shi ta ci gaba da aiki, ta yadda za a kare Kwankwaso da mukarrabansa daga yiwuwar kamawa da gurfanarwa a gaban kuliya.