Mai shari’a Maryann Anenih ta Kotun babban birnin tarayya ta ƙi amincewa da neman belin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya gabatar, tana mai cewa an gabatar da shi ne kafin lokacin da ya dace.
A cikin hukuncin, Mai shari’a Anenih ta ce, saboda an gabatar da neman belin lokacin da Yahaya Bello bai kasance a riƙe ba ko a gaban kotu ba, wannan neman belin ba shi da inganci.
Tsohon gwamnan yana fuskantar tuhuma tare da wasu mutane biyu bisa zargin aikata laifin sama faɗi da kuɗi da ya akai Naira biliyan 110 da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gabatar masa.
A cikin hujjar da lauyan wanda ake tuhuma, JB Daudu (SAN), ya gabatar, ya roƙi kotu da ta ba da belin, yana mai cewa Bello zai kiyaye sharuɗɗan belin.
Mai gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro, ta bayyana cewa neman belin ya karya ƙa’ida domin an gabatar da shi kafin a gurfanar da wanda ake tuhuma. Mai shari’a Anenih ta kuma tabbatar da cewa daga cikin dokar ACJA, ana iya gabatar da neman belin bayan an kama wanda ake tuhuma, an yi masa rajista ko an kawo shi a gaban kotu.