Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Jos ta Filato a ranar Juma’a ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Hon. Moses Sule.
Kakakin wanda dan jam’iyyar PDP ne, kotun ta koreshi tare da Danjuma Azi, mamban da ke wakiltar mazabar Jos ta Arewa Maso Yamma a majalisar dokokin jihar.
- PDP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Zaben Kaduna Da Ta Tabbatar Da Nasarar Uba Sani
- An Lakadawa Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya Duka A Kano
Kazalika, kotun ta ayyana tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Naanlong Daniel and Hon. Mark Na’ah, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
Mai korafin ya kalubalanci daukar nauyin takarar Sule da Azi ne bisa dalilin cewa jam’iyyar PDP ba ta dace ta kasance a cikin masu neman zaben ba bisa dalilin cewa jam’iyyar ba ta da tsari.
A hukuncinta, kotun karkashin jagorancin Muhammad Tukur, ta ce, PDP ba ta cancanci daukan nauyin wadanda ake kara ba domin su shiga neman zaben ba.
Kazalika, kotun ta ce, PDP ta nuna rashin mutunta Mai Shari’a S.P Gang na babban kotun jihar Filato da ya yanke hukunci a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2020 da ya umarci jam’iyyar ta gudanar da zabukan cikin gida a gundumomi.
Mai Shari’a Tukur ya ce, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kasa gabatar da wani shaidar na sahihin takarda da zai nuna cewa jam’iyyar ta PDP ta sake gudanar da babban taronta na cikin gida a 2021, kamar yadda wanda ake kara suka yi ikirari.
A dai ranar Alhamis ne kotun da ke karkashin mai shari’a Tukur ta kori wasu mambobin jam’iyyar PDP biyu wanda suka kasance ‘yan majalisun dokokin jihar.