Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage ci gaban shari’ar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan zuwa ranar 4 ga Fabrairu 2026, bayan zaman da aka shirya yau Litinin ya ci tura saboda rashin halartar mai shari’a Mohammed Umar. Wannan dai shi ne karo na biyu da ƙarar ke kasa ci gaba, kasancewar a ranar 21 ga Oktoba ma shari’ar ta tsaya ne sakamakon zanga-zangar da Omoyele Sowore ya jagoranta kan neman sakin Nnamdi Kanu. Tun a ranar 22 ga Satumba ne alƙalin ya tsara ci gaban zaman, amma suka tsaya bayan lauyanta ya ƙalubalanci ci gaba da shari’ar.
Sanata Natasha na fuskantar gurfanarwa ne tun a ranar 30 ga Yuni kan tuhume-tuhume shida da ofishin babban mai shigar da ƙara ya gabatar.
- Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha
- Natasha Ta Jinjinawa ‘Yan Mazaɓarta, NLC, NBA Bayan Ta Koma Ofishinta Na Majalisa
An bada belinta, sannan aka ware Satumba 22 don fara sauraron shaidu. Sai dai a ranar da aka koma kotu, lauyan gwamnati ya shirya fara gabatar da shaida bayan sanya allon talabijin a ɗakin shari’a, amma lauyanta, Ehiogie West-Idahosa, ya dage cewa kotu ba za ta iya ci gaba da sauraron shari’ar ba saboda sun riga sun shigar da ƙarar ƙalubalantar hurumin kotu. Ya ce matsalar ba a kan tuhume-tuhumen bane kai tsaye, amma a kan abin da ya kira amfani da ikon Babban Lauyan Kasa ba bisa ƙa’ida ba.
Lauyan ya kuma koka cewa ba a miƙawa bangarensu kwafin bayanan shaidun gwamnati ba, abin da ya saɓawa yadda ake yanke shawara cikin adalci. Duk da cewa lauyan gwamnati David Kaswe ya nemi kotu ta ci gaba da shari’a, mai shari’a Umar ya dage cewa dole ne a fara sauraron wannan ƙalubale kafin komawa ga shaida. Alƙalin ya ce dole ne kotu ta fara yanke hukunci kan ikon da ake ƙalubalantarta, kafin a bi mataki na gaba a cikin shari’ar.
A cikin takardar tuhume-tuhumen, ana zargin Sanata Natasha da aikawa da bayanan karya da ke iya cutarwa ta hanyar sadarwa da nufin tayar da hankula da jefa rayuka cikin haɗari.













