Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ki amincewa da ba da belin Abba Kyari da wasu mutane hudu da ake zargi da safarar hodar Ibilis.
Kyari, wanda mataimakin kwmaishinan ‘yansanda da mutanen hudu suna fuskanatar shari’a ne kan safarar miyagun kwayoyi da NDLEA ke musu.
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano Za Ta Rushe Gine-Ginen Da Aka Yi A Hanyar Magudanan Ruwa
- Buhari Zai Sake Ciyo Bashin N11trn Don Cike Gibin Kasafin Kudin 2023
A watan Maris ne NDLEA ta gurfanar da Kyari da wasu mutane shida a gaban kotu bisa zarge-zargen da suka shafi ta’amali da hodar iblis.
An gurfanar da shi tare da ‘yansanda huɗmdu da aka dakatar ciki har da ACP Sunday Ubia, ASP James, Inspekta Simon Agirigba da kuma Inspekta John Nuhu.
Yayin zartar da hukuncin, mai shari’a Emeka Nwite, ya ce masu karar sun gaza gabatar da isassun hujjoji da za su bai wa kotun kwarin gwiwar ba su beli.
Mai shari’a Nwite ya kuma jaddada hukuncin da ya yi na ranar 8 ga watan Maris, inda ya bukaci a hanzarta sauraron karar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp