Wata kotun shari’a a jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin tsare wani matashi dan shekara 29, a gidan gyaran hali kan zargin satar wata tunkiya da ta kai Naira 27,000.
Ana tuhumar matashin da ke zaune a Sani Manage Quarters Kano da laifin sata.
- Zabe: Kotun Kano Ta Kwace Kujerar Datti Ta Baiwa Iliyasu Kwankwaso
- An Kaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana’o’i A Kano
Alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Satumba.
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, Insp Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wani mutum mai suna Sabo Iliyasu, ne ya shigar da kara, ya kai karar ne a ranar 11 ga watan Satumba a ofishin ‘yan sanda na Mandawari.
Wada ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa cikin rumfar wanda ake zargin da ke unguear Sani Mainage ya sace masa Tunkiya daya.
Ya lura cewa wanda ake tuhumar ya kai Tunkiya zuwa wani ginin kwango da ba a kammala ba ya yanka.
Lokacin da aka karanta wa wanda ake tuhuma tuhumar, ya musanta aikata laifin.