Kotun majistire ta biyu da ke titin Daura cikin jihar Kaduna ta bayar da umarnin a kamo Abdullahi Suleiman, Babban Dogarin tsaron gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i.
Lauyan da ke tsaya wa wadda ta shigar da karar dogarin a gaban kotun ta Majistare, Barista Abubakar A Ashat a hirarsa da manema labarai a harabar kotun jim kadan bayan Kotun ta saurari karar ya ce, Shari’o’i biyu ne a gaban Kotun da mai karar Fiddausi Abudulahi ta shigar a kan dogarin na gwamnan na ya fasa mata bululuwanta da ke cikin filinta a Unguwar Danhono.
- An Cimma Sakamako Guda 1339 Yayin Taron CIFTIS
- Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Riba Ce Ga Kasashe Masu Tasowa
Ya ce, a wannan shari’ar ta farko, Abudulahi ya bukaci da mu zauna mu yi sasanci, kan maganar filin, mun je mun zauna, amma ba a samu masalaha ba.
Ya ci gaba da cewa, a zaman da kotun ta yi mun shaida mata cewa, za a ci gaba da shari’ar saboda ba a sansanta ba.
Haka nan Lauyan wanda ake karar shi ma bai halarci zaman kotun ba, shi ma Abdullahi bai halarci zaman ba.
Ashat ya kara da cewa, sakamakon hakan ne kotun a bayar da umarnin a kamo wadanda ake karar.
Ya ci gaba da cewa, sashe na 228 na kundin gabatar da Shari’a na jihar Kaduna ya tanadi cewa, duk wanda ake tuhuma a gaban kotu, dole ne ya kasance yana kotu sai dai idan Kotun ce ta ce kar ya zo gabanta.
Ya ce, kotun ta sa ranar 14 ga watan Satumbar 2022 don ci gaba da karar.
Ya ce, haka kotun ta kuma kori takardar da dogarink ya gabatar a gabanta ta kalubalantar cewa, kotun ba ta hurumin sauraron karar.