Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Umarci ’Yan Sanda Su Biya Diyyar Rayukan Mabiya Sheikh El-Zakzaky

Published

on

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja, a jiya Litinin ta umarci ’yan sanda da su biya diyyar Naira milyan 15 a kan zargin kisan da su ka yin a wasu ’yan kungiyar IMN su uku.

Mai shari’a Taiwo Taiwo, a cikin hukuncin da ya zartar ya kuma umurci asibitin kasa da ke Abuja da ya hanzarta sakin gawarwakin ’ya’yan kungiyar uku da su ke ajiye a dakin ajiye gawarwaki na asibitin.

Mai shari’a Taiwo, a lokacin da ya ke yanke hukuncin ya ce kowane guda daga cikin mutanan uku da aka kashe tilas ne a biya naira milyan biyar a matsayin fansar kisan da aka yi ma sa.

Sai dai alkalin bai amince da bukatar da aka shigar a gabansa ba wacce ke neman kotun ta umurci ‘yan sandan da su nemi gafara a jaridun kasar nan biyu masu fitowa kullum-kullum.

An zargi ‘yan sandan ne da kisan Suleiman Shehu, Mahdi Musa, Bilyaminu Abubakar Faska da Askari Hassan a lokacin da su ke gudanar da wata zanga-zangar lumana ta neman a saki shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa, a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Wadanda su ka shigar da karar, da a ka ce su ’yan uwan mamatan ne, a cikin karar sun hada da Ibrahim Abdullahi, Ahmad Musa, Yusuf Faska da Said Haruna.

Sai dai a duk tsawon lokacin da a ka dauka a na tafka shari’ar a kotun, rundunar ‘yan sandan ba ta shigar da wata bukatar kalubalantar karar tasu a gaban kotun ba, ba ta kuma turo wani lauya da zai tsaya ma ta ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: