Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano, ta wanke Kwamishinan Ma’aikatar Harkoki ka Musamman na Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara, daga zargin aikata zina da matar aure, Tasleem Baba Nabegu.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama Sankara tare da Tasleem a wani kangonsa da yake aikin ginawa, amma alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya yanke hukunci cewa binciken ‘yansanda ya kasa samun wata shaida da ke nuna an aikata laifin.
- Dan Nijeriya Lookman Na Kan Gaba Wajen Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika Ta Bana
- Shugaba Xi Jinping Ya Ce Kasar Sin Da Birtaniya Na Da Dimbin Sararin Yin Hadin Gwiwa
Alkalin ya kuma bayyana cewa wanda ya shigar da kara, Nasiru Buba, da lauyoyinsa ba su halarci zaman kotun ba, don haka dole ya yi watsi da karar.
Lauyan Sankara, Barista Sadam Suleiman, ya ce hukuncin ya dawo da martabar wanda yake karewa.
A bangare guda, wakilin Tasleem, ya nuna yiwuwar daukar matakin shari’a kan Nasiru Buba saboda bata mata suna.
Alkalin kotun, ya jaddada bukatar gudanar da bincike mai zurfi a kan zarge-zargen da suka shafi manyan mutane domin kaucewa tafka abin kunya.