Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta wanke Hon. Gbenga Makanjuola da Kolawole Shittu, tsohon hadiman tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, daga zargin damfara ta ₦3.5 biliyan.
Makanjuola ya nuna jin daɗinsa da godiyarsa bayan hukuncin, inda ya bayyana wahalhalun da suka sha tsawon shekaru takwas. Ya ƙara da cewa hukuncin Kotun Ƙolin na baya-bayan nan ya tabbatar da halaccin kuɗin da ake magana akai, wanda ya kawo ƙarshen tuhume-tuhumen laifuka a kansa.
- Rikicin Sarautar Kano: Yadda Gwamnatin Abba Ta Sauya Alkibla
- Abba Ya Sake Nada Tsohon Sarkin Gaya Da Wasu Sabbin Sarakuna A Kano
Hukuncin kotun ya zo ne bayan da manyan lauyoyin da suka wakilci Makanjuola da Shittu suka yi bayani cewa kuɗin na cikin sahihin ciniki na kasuwanci. Lamarin ya fara ne tun shekarar 2018 lokacin da hukumar EFCC ta tuhumi su da wasu da laifin haɗin baki, safarar kuɗi da kuma biyan kuɗi ba tare da amfani da cibiyoyin kudi da aka aminta da su ba.
Da farko, EFCC ta zargi waɗanda ake tuhuma da haɗa baki don boye asalin kuɗin da kuma biyan wasu manyan kuɗaɗe ba tare da amfani da cibiyoyin kudi ba.
Kotun ta yanke cewa tuhumar ba ta da inganci. A watan Janairun 2021, EFCC ta sake gabatar da tuhumar, amma daga ƙarshe kotun ta wanke waɗanda ake tuhumar bayan bin tsari na shari’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp