Wata babbar kotun Jihar Yobe da ke garin Pataskum ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan jami’in sojan nan Lance Corporal John Gabriel da ya kashe fitaccen malamin addinin Musuluncin jihar, Sheikh Bagoni Aisami.
Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ga abokin aikin sojan mai suna Lance corporal Adamu Gideon da ya taimaka wajen aikata kisan.
- Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai
- An Bayyana Rawar Da Kasar Sin Ta Taka Kan Sauyin Yanayi Yayin Taron COP28
A hukuncin da ya zartar a ranar Talata, Alkalin kotun, mai shari’a Usman Zanna Mohammed, ya ce kotu ta samu John Gabriel da laifin kisan kai, shi kuma Adamu Gideon da laifin taimakawa wajen hadin bakin aikata laifin.
Alkalin kotun ya ce mutanen biyu sun kasa tabbatar wa kotun cewa ba su da laifi, don haka aka yanke musu hukunci daidai da laifinsu.
Idan za a iya tunawa a watan Agustan 2022 ne aka kama jami’in sojan bisa zargin yi wa sheikh Goni Aisami kisan gilla a wani wuri da ke yankin Karamar Hukumar Karasuwa a Jihar Yobe, kusa da garin Gashua bayan da malamin ya ragewa sojan hanya a motarsa daga garin Nguru.
A baya dai an yi ta jan kafa wajen gudanar da shari’ar da ta kai har sai da iyalai da daliban malamin da kungiyoyin fararen hula suka yi ta kokawa.
Lamarin kisan malamin ya bar baya kura musamman a Arewacin Nijeriya inda aka dinga kiranye-kiranye kan hukunta wadanda suka aikata laifin.