• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatun Akpabio Kan Dakatar Da Sanata Natasha

by Sadiq
5 months ago
Kotu

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe guda biyu da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar dangane da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka, ta umarci Sanata Akpabio da ya biya Sanata Natasha tara Naira 100,000.

  • Wang Yi Ya Gabatar Da Jawabi Albarkacin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” Karo Na Farko Na MDD
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Kogi Ta Gargadi Siyasantar Da Kalubalen Tsaro A Jihar

Kotun ta bayyana cewa ta amince da buƙatar Akpabio na janye ƙorafe-ƙorafen biyu da ya shigar ranar 20 da 25 ga watan Maris, 2025.

Sai dai bayan janyewar, kotun ta kori ƙorafe-ƙorafen gaba ɗaya kuma ta bayar tara ga wanda ake ƙara na farko (wato Sanata Natasha).

Hakazalika, kotun ta ce za a goge lambar ƙarar daga kundin shari’a.

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Akpabio ya shigar da buƙatu a gaban kotun inda ya nemi ƙarin lokaci don ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Maris, 2025.

Wannan shari’a ta haɗa da Sanata Natasha da ke ƙarar Sakataren Majalisar Tarayya da wasu mutane uku kan dakatar da ita.

Haka kuma, Akpabio ya nemi kotu ta ba shi izini ya ɗaukaka ƙara da kuma dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar a Babbar Kotun har sai an yanke hukunci a kotun ɗaukaka ƙara.

Sai dai yanzu da aka janye ƙorafe-ƙorafen kuma kotu ta yi watsi da su, hakan na nufin waɗannan bukatu na Akpabio ba za su ci gaba da sauraron su a a kotun ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro
Manyan Labarai

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Next Post
Tinubu Ya Ceto Nijeriya Daga Faɗawa Matsin Tattalin Arziƙi – Gwamna Namadi

Tinubu Ya Ceto Nijeriya Daga Faɗawa Matsin Tattalin Arziƙi – Gwamna Namadi

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

October 27, 2025
An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Kotu

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.