Wata ta musamman da ke Ikeja ta sanya ranar 12 ga Disamba domin sauraron ɓangaren tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele, wanda ke ƙalubalantar ikon kotun kan sauraron shari’arsa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Emefiele ya tunkari Kotun ɗaukaka ƙara yana mai ƙalubalantar ikon kotun kan sauraron tuhumar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gabatar masa na yin amfani da muƙaminsa wajen aika badaƙaloli masu yawa.
Emefiele na fuskantar tuhuma kan zargin amfani da muƙaminsa ta hanya maras kyau tare da aikata almundahanar kuɗi na dala biliyan 4.5 da Naira biliyan 2.8. Tsohon abokinsa, Henry Omoile, shi ma na fuskantar tuhumar karɓar kyaututtuka daga jami’ai ba bisa ƙa’ida ba.
A lokacin da aka ci gaba da shari’ar a ranar Talata, lauyan EFCC, Mr. Rotimi Oyedepo (SAN), ya sanar da kotu cewa Kotun ɗaukaka ƙarar ta yi hukunci a kan neman Emefiele a ranar 29 ga Nuwamba, inda ta umurci kotun ƙasa da ta saurari wannan neman kafin ta ci gaba da shari’ar.