• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Muhammadu Iliyasu Bashir A Matsayin Sarkin Gwandu

by Umar Faruk
2 days ago
in Labarai
0
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Muhammadu Iliyasu Bashir A Matsayin Sarkin Gwandu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar da aka daɗe ana yi tsakanin Sarkin Gwandu na yanzu, Muhammadu Iliyasu Bashir, da tsohon Sarki, Al-Mustapha Haruna Jakolo.

A hukuncin da kotun ta yanke, ta soke hukuncin kotun Jihar Kebbi da kotun ɗaukaka ƙara da ke Sakkwato, waɗanda suka umarci a mayar da Jakolo a matsayin Sarkin Gwandu watanni shida da suka wuce.

  • Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Kotun Ƙoli ta karɓi ƙarar da Sarkin Gwandu mai ci da gwamnatin Jihar Kebbi suka ɗaukaka, inda ta bayyana cewa Muhammadu Iliyasu Bashir shi ne sahihin Sarkin Gwandu.

Alƙalai biyar ne suka saurari shari’ar, inda uku daga cikinsu suka yarda da hujjojin da lauyoyin Sarkin Gwandu da gwamnatin jihar suka gabatar.

Sai dai sauran alƙalai biyu sun goyi bayan hujjojin da lauyan Jakolo ya gabatar, amma alƙalai ukun sun rinjaye su.

Labarai Masu Nasaba

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Wannan rikici na kujerar mulki ya ɗauki kusan shekaru 20 ana kai ruwa rana a kotu.

Yanzu dai hukuncin kotun ƙoli ya kawo ƙarshen shari’ar, inda ta tabbatar da Muhammadu Iliyasu Bashir a matsayin Sarkin Gwandu na Ashirin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KotuSarkin Gwandu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai

Next Post

Hajjin 2025: Alhajin Kano Ya Rasu A Makka Kwana Ɗaya Kafin Arfa

Related

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC
Labarai

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

1 hour ago
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi
Labarai

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

2 hours ago
Daurarru
Labarai

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

11 hours ago
Wutar lantarki
Labarai

Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

13 hours ago
Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka
Labarai

Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

14 hours ago
Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano
Manyan Labarai

Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano

15 hours ago
Next Post
Hajjin 2025: Alhajin Kano Ya Rasu A Makka Kwana Ɗaya Kafin Arfa

Hajjin 2025: Alhajin Kano Ya Rasu A Makka Kwana Ɗaya Kafin Arfa

LABARAI MASU NASABA

Adawa

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

June 7, 2025
2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

June 7, 2025
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

June 7, 2025
Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

June 6, 2025
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

June 6, 2025
Daurarru

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

June 6, 2025
Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

June 6, 2025
Wutar lantarki

Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

June 6, 2025
Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

June 6, 2025
Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano

Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano

June 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.