Kwanaki kadan bayan soke zaben kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, ta sake soke zaben mataimakin kakakin majalisar, Jamilu Umaru Dahiru Barade na jam’iyyar PDP.
Kotun mai Alkalai guda uku, a hukuncin da ta yanke a ranar Litinin din da ta gabata, sun yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, wadda tun farko ta tabbatar da zaben Barade a matsayin zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya.
- Yakin Zirin Gaza: An Kara Kwanaki Biyu Na Tsagaita Bude Wuta
- Kasafin Kuɗin 2024: A Jihar Katsina, Ɓangaren Noma Zai Samu Kashi 6.21% Kawai – Kwamishina.
Don haka, alkalan sun bayar da umarnin sake gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe na mazabar, inda mai shigar da kara na jam’iyyar APC, Aliyu Abdullahi Ilela, ya yi zargin cewa an yi aringizon kuri’u.
Kotun ta umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta karbo takardar shaidar cin zabe da aka baiwa mataimakin shugaban majalisar tare da sake gudanar da zabe a rumfunan zaben da abin ya shafa kafin sake tantance wanda ya yi nasara.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, hukuncin ya zo ne kwanaki kadan bayan da kotun daukaka kara ta soke zaben Kakakin Majalisar, Abubakar Sulaiman.