Kotun daukaka kara ta Kano ta sanya ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, 2023, domin sauraren karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya shigar, yana kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar da ta tsige shi a matsayin gwamnan jihar.
Kotun daukaka kara, a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, ta nuna cewa za a fara sauraren karar mai lamba CA/KN/EP/GOV/KAN/34/2023 a ranar Litinin a kotun daukaka kara da ke Abuja.
- Gwamna Uba Sani Ya Bayar Da Umurnin Gaggauta Biyan Kudin Wutar Lantarki Na Jami’ar KASU
- Sake Bude Iyaka: Matsalar Da Manoman Arewacin Nijeriya Za Su Fuskanta
Wadanda ke cikin karar sun hada da Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP da kuma jam’iyyar adawa ta APC, da dan takararta, Nasir Gawuna, da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Idan dai za a iya tunawa dai kotun ta yanke hukuncin ne, inda ta bayyana dan takararta APC, Gawuna a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
Kotun ta soke zaben Gwamna Yusuf ne bayan soke kuri’unsa 165,663, inda ta ce INEC ba ta sanya hannu ko tambari ba akan kuri’unsa.
Idan za a tuna cewa INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris bayan ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da abokin hamayyarsa Gawuna ya samu kuri’u 890,705.
Sai dai kotun sauraron kararrakin zabe ta soke kuri’u 165,663 daga kuri’un Yusuf, wanda ya sa kuri’unsa suka koma 853,939, wanda hakan ya sa Gawuna ya ba shi tazarar kuri’u 30,000.
Sakamakon haka ne, kotun ta bayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna tare da umartar INEC da ta janye takardar shaidar cin zaben Yusuf tare da bai wa Gawuna na jam’iyyar APC.
Sai dai Gwamna Yusuf da jam’iyyarsa, NNPP da kuma INEC sun garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke.