Kotun Kasar Masar Ta Yanke Wa Wasu Magoya Bayan Mursi Hukunci Kisa

Supporters of the Muslim Brotherhood and ousted Egyptian President Mohamed Mursi take part in a protest against the military and interior ministry in the southern suburb of Maadi, on the outskirts of Cairo November 1, 2013. U.S. Secretary of State John Kerry will visit Egypt a day before deposed Islamist President Mohamed Mursi goes on trial, the next likely flashpoint in the struggle between his Muslim Brotherhood and the army-backed interim government. Several hundred Islamists protested in a few cities on Friday, responding to a call from a pro-Mursi alliance for daily protests until the ousted president stands trial on Monday. The "Rabaa" or "four" gesture is in reference to the police clearing of Rabaa al-Adawiya protest camp on August 14. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) - RTX14WMN

Wata kotun Masar ta yanke wa ‘ya’yan kungiyar ‘Yan uwa Musulmi wato Ikhwan al-Muslim su 24 hukuncin kisa bayan ta same su da laifin kashe jami’an ‘yan sanda. Wata Jarida mallakin gwamnati, a wani rahotonta ta ce kotun manyan laifuka da ke yankin Damanhour ta yanke hukuncin kisan kan mutum 16 da ta ce suna da alaka da kungiyar ‘Yan uwa Musulmi, ciki har da Mohamed Sweidan, wanda shi ne jagoran kungiyar a yankin, domin ta same su da laifin jefa bam a cikin wata motar ‘yan sanda a birnin Rashid da ke jihar Beheira a 2015.

Wannan kotun ta kuma yanke wa wasu mambobin kungiyar su takwas hukuncin kisa, wadanda su kuma aka same su da laifin kashe wani dan sanda a watan Disambar 2014 a birnin Ad Dilinjat da ke jihar ta Beheira.

Sai dai takwas cikin wadanda aka yanke wa hukuncin ba sa hannun hukuma domin tuni su ka tsere.

Exit mobile version