Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su guji duk wani abu da zai iya haifar da rashin zaman lafiya biyo bayan zaman kotun koli kan zaben gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairu.
Hakan ya biyo bayan wata yarjejeniyar zaman lafiya da shugabannin jam’iyyun biyu suka sanya wa hannu a gaban jami’an tsaro a jihar a ranar Litinin a Lafiya.
- Mutane Kalilan Ne Suka Sace Dukiyar Nijeriya Ta Hanyar Tallafin Mai – TinubuÂ
- Muna Bukatar Dala Biliyan 1 Don Ceto Rayuka A 2024 – WHO
Wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar APC na jihar, Mista Otaru Douglas, ya raba wa manema labarai, ta bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da magoya bayanta da su aiwatar da duk wani abu da ya shafi murna ko nuna goyan baya cikin salama ba tare da cin mutunci ko cin zarafi ba.
Kotun koli dai ta sanya ranar Talata 16 ga watan Janairu domin sauraron karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Mista David Ombugadu, ya shigar kan hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben Abdullahi Sule a matsayin halastacen gwamnan jihar.