Kotun koli ta kaddamar da alkalai bakwai da za su saurari koken da ‘yan takarar shugaban kasa suka shigar a gabanta na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabirairun 2023.
Bugu da kari, an gabatar da kwafi ga masu karar Atiku Abubakar, dan takakar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da na jam’iyya LP Peter Obi da kuma Chichi Ojei ta jam’iyyar APM.
- Tinubu Ya Naɗa Sababbin Shugabannin Hukumomin Yaɗa Labarai
- An Dakatar Da Shugaban Jam’iyyar APC A Jigawa Kan Zargin Fyade
Magatartar kotun, Zainab M. Garba wadda ta rattaba hannu a kwafin ta bayyana cewa, bisa sashen doka ta da ta 1(2) na kotun ta shekarar 1985 da aka sabunta, ya wajaba a bai wa masu karar kwafin.
Kazalika, jerin sunyayen alkalan su ne, Musa Dattijo Muhammad, Uwani Musa Abba Aji, Lawal Garba, Helen M. Ogunwumiju, I.N. Saulawa, Tijjani Abubakar da kuma Emmanuel Agim.
Bugu da kari, Atiku cikin takardar daukaka karar da ya gabatarwa da kotun ya ce, kotun sauraron karar zaben ta yi kuskure akan fatalin da ta yi da karar da ya gabatar mata, akan gazawarsa na tabbatar wa da kotun hujja akan zargin tafka magudi a zaben shugaban kasa, na samun kuri’u kashi 25 a birnin tarayyar Abuja da kin biyan diyyar dala 60,000 da kuma gazawar INEC na tura sakamakon zaben da aka karbo daga mazabun da aka jefa kuri’u zuwa a cikin na’urar BVAS, kamar yadda doka ta tanadar.
Kazalika, bababan Lauya (SAN) Chris Uche da ke mai tsaya wa Atiku a takardar da ya gabatar wa da kotun ya kuma gabatar wa da kotun zargin shedar kammala makaranta na Tinubu, bisa cewa na bogi ne.
Bugu da kari, a bangaren Obi kuwa yana jayayya ne akan yadda kotun sauraron kararrakin zaben ta ki amincewa da samun nasararsa a mazabu 18,088.
Ita kuwa Ojei ta jam’iyyar APM, a nata korafin ta nuna jayayya ne akan Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima kan cewa, a soke zabensu.
Sai dai, martanin da Tinubu ya mayar ta hanyar babban Lauyansa Wole Olanipekun (SAN) mai tsayawa ya bukaci kotun da dauki koken Atiku a matsayin cin mutuncin kotu.
Kazalika, Tinubu ya danganta korafin Obi matsayin mara tushe da hujja.