Kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jami’yyar NNPP a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Kano.
Kotun ta warware hukuncin da kotun sauraron kararrakim zabe da kotun daukaka kara suka zartar a baya.
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Bala Mohammed A Matsayin Gwamnan Bauchi
- Shari’ar Kano: Gwamna Yusuf Da Mataimakinsa Sun Halarci Zaman Kotun Koli
Kwamitin alkalai guda biyar sun ce hukuncin da kotun kasa ta yi na soke kuri’u 165,616 Gwamna Yusuf na daidai ba ne.
Hukuncin da mai shari’a Inyang Okoro ya yanke ya kuma ce batun zama dan jam’iyya na Gwamna Yusuf wannan hurumin jam’iyya ne.
Ya ce binciken da suka yi karkashin sashe na 177 (c) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da sashe na 134 (1) na dokar zabe, babu hujja da ta nuna Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne.