Bello Hamza" />

Kotun Rasha Ta Ki Bada Belin Paul Whelan

Wata Kotun a Rasha ta ki bada belin wani ba-Amurke da ake zarginsa da laifin leken asiri.
Paul Whelan, wanda ke zaman dan kasashen Amurka da Biritaniya, tsohon soja ruwa a Amurka ne da aka kama shi ran 28 ga watan Disamaba bayan da hukumar tsaron kasar Rasha ta zarge shi da laifin leken asirin kasa, koda yake kuma hukumomin Rasha din ba su bayyana ainihin laifin da ake zarginsa da aikatawa ba. Iyalansa sun ce ba shi da wani alifi.
Mutumin dan shekaru 48 ya bayyana a kotu a birnin Moscow a yau Talata, yana neman a sake shi, amma alaalin ya ai amincewa da hakan.

Exit mobile version