Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto, a ranar Asabar, ta tabbatar da zaben gwamna Ahmed Aliyu.
Kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Saidu Umar, suka shigar gabanta, inda suke kalubalantar nasarar da jam’iyyar APC da dan takararta Ahmed Aliyu suka samu a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Mutum 4, Da Sace 18 A Harin Da Suka Kai A Wani Kauye A Sokoto
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe Biliyan 20.3 Domin Sayen Abinci Da Wasu Ayyuka
A cewar kotun mai Alkalai uku bisa jagorancin Alkalin Kotun mai shari’a, Haruna Mshelia, ya jagoranta ya ce wadanda suka shigar da karar sun gaza kare karar da suka shigar a gaban Kotu.
LEADERSHIP ta rawaito cewa tun da farko ‘yan jaridar da suka isa harabar kotun da karfe 7:00 na safiyar ranar Asabar an hana su shiga Kotun kuma an tsauraran matakan tsaro a harabar kotun, dalilan da suka sanya shiga harabar kotun ya yi wa ‘yan jarida wuya.
Wani jami’in DSS a lokacin da yake jawabi ga ‘yan jarida a kotun ya ce ‘yan jaridar da ke aiki da kafafen yada labarai mallakar gwamnati ne kadai za su samu damar shiga harabar kotun.