Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa na Kasa (RIFAN) reshen Jihar Kano, ALHAJI ABUBAKAR HARUNA ALI YAU, ya sami tattaunawa da Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, inda wannan tattaunawar an yi ta ne dangane da bai wa mutane basukan kayan noma, amma kuma biyan ya gagara. Wannan ya sa muka leka, domin jin irin matakan da wannan kungiyar za ta dauka. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Akwai mutanen da ku ka bai wa bashin noma da alama wasu sun ci kuma sun ki biya, wanne kira ka ke yi wa irin wannan mutane domin su dawo da abin da suka ranta?
To gaskiya abin da zan ce shi ne mutanenmu na Arewa ba su da cika alkawari domin ba ma son biyan bashi, kuma wannan kudi mu muka je muka ciyo bashi a babban bankin kasa wato CBN, dalilin karbar wannan bashi domin mutanenmu su fita daga halin da suke ciki, amma sun karba sun yi shiru kuma shi wannan babbabn banki ya ce lallai mu dawo masa da duk kudin da muka karba.
Mutane masu karbar wannan bashi baka ganin cewa gani suke yi duk wanda ya ci gani yake ya ci banza saboda na gwamnati ne?
Eh, to! Koma dai me mutum za ice ya sani, kafin ka karbi wannan kaya an gaya maka bashi ne, akasarinmu duk musulmi ne kuma kowa ya san illar bashi a Musulunci saboda haka mutane suna daukar wannan abin da wasa kuma bashi ne ko bayan ranka ana binka wannan bashi. Wannan ana yi ne domin tattalin arzikin kasar nan ya karu, wannan shi ne yanzu irin wannan sace-sace da ake ta fama da shi, ita gwamnati tana yin wannan ne domin ta rage zaman banza, idan kana samun irin wannan tallafin yaushe za ka shiga irin waccan harka, ka ga ba zai yiwu ba.
Idan ya zamana ana karba ba’a biya, wane sakamako lamarin zai bayar?
Gaskiya abubuwa za su kara lalacewa, kuma bari na baka misali, lokacin da aka shiga cutar Korona wanda ta wuce, wannan lokacin da ba mu da abinci a kasar ai da an shiga mummunan hali kuma wannan harka shekararmu uku muna ba da wannan bashin adaidai wannan lokacin kasar ta shiga jerin kasashe masu noma shinkafa kuma ita kanta kasar a baya tana kashe makudan kudi wajen shigo da shinkafa, na wajen tiriliyan daya a duk lokaci, amma wannnan lokaci duk wannan kudi suna nan gida ba a kai su ko’ina ba. Amma mutane gani suke yi sun ci banza wallahi ba wannan maganar dole a biya.
Wato duk wanda ka ga mun ba wannan kaya sai ya kai mun ga gonarsa tukunna, kuma su mutananmu akwai dabara sosai, idan an toshe can sai su bude can. Ganin haka mutane duk wanda za mu ba wa wannan bashi sai an je kashi biyu, sannan za mu ba shi, kai sanda ka zo karbar wannan bashi ka zo da hotanka da BBN dinka da lambar wayarka. To ta ina zaka gudu komai naka yana wajanmu. To an baka bashin 100,000 wani ya karba ya baka 20,000. Wannan ba daidai bane.
Wane mataki za a dauka domin dawo da wannan kudin kenan?
To, za mu koma da duk wannan hotunan mutanen da suka ci wannan bashi zuwa ga hukuma domin su dawo da kudin.