Daga Hussaini Yero,
Gwamna Jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawalle Maradun, ya ba wa ’yan bindiga masu garkuwa da mutane wa’adin wata biyu da su ajiye makamansu ko kuma su gamu da fushin jami’an tsaro.
Matawallen Maradun ya bayyana haka ne a jiya Talata da yamma lokacin da ya ke yi wa al”ummar jihar jawabi a kan matsalar tsaro da ta addabi jihar tasa.
Hon Matawalle ya bayyana cewa, bayan sako dalibai mata na sakandiren Jangebe da aka sace a ranar 26 ga Fabrairu, 2021, ya samu ganawa da Shugaban Kasa Muhammad Buhari akan lamarin.
Ya bayyana cewa, Shugaban Kasa ya sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama da hakar ma’adanai ba tare da izini ba a fadin jihar ta Zamfara kuma wannan dokar nan daram, inda duk wanda ya saba ma ta, zai gamu da fushin jami’an tsaro.
Haka kazalika, Matawalle ya tabbatar da cewa, Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya aminta da sulhu ga masu son sulhun, amma wadanda ba sa son sulhu, lallai za a tarwatsa su a duk inda suke a fadin jihar.
“Don haka muka ba wa ’yan bindiga wa”adin wata biyu da su mika makamansu da gaggawa ko kuma su gamu da fushin jami’an tsaro,” inji shi.
Gwamna Matawalle ya kuma bayyana wasu dokoki da za su fara aiki nan take, don ganin an magance matsalar tsaro a fadin Jihar, yana mai cewa, duk dan siyasa da aka samu da hannu wajen kawo matsalar matsalar tsaro zai gamu da hukunci, kuma sarakuna da shugabannin Kananan Hukumomi dole ne su zauna a garuruwansu, don sanin masu shiga da fice.
Kuma batun hawa babur mutum uku da kuma jerin gwanon mashina haramun ne a fadin Jihar ta Zamfara. Ya kara da cewa, haramcin ‘yan sa-kai da ayyukansu ya na nan daram da kuma yawo da makamai.
“Duk wanda ya ki bin wadannan dokokin, lallai zai gamu da fushin jami’an tsaro,” inji Gwamna Matawalle Maradun.