Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar yankin Neja-Delta da su kasance masu hakuri da mutuntawa, suba wa gwamnati damar gudanar da ayyuka na cigaban al’ummar yankin.
Shugaba Buhari ya yi wannan roko ne a yau Laraba a Abuja a wajen bude taron kwana biyu na gudanarwa da ma’aikatar harkokin Neja Delta ta shirya a fadar shugaban kasa, Villa Abuja.
Shugaban Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Sufuri, Muazu Jaji Sambo, ya bayyana shirin gwamnatin na shimfida ayyuka don inganta rayuwar mutanen yankin, na samar musu da sabuwar rayuwa.
A cewarsa, gwamnatinsa ta shirya tsaf wajen aiwatar da wasu tsare-tsare da nufin samar da ingantacciyar yankin Neja-Delta.
Shima da yake jawabi, Gwamna Hope Uzodinma yace kiran na shugaba Buhari zai kawo cigaban yankin Neja Delta da ake bukata.