Gwamnan jihar Adamwa Ahmadu Umaru Fintiri, ya umurci shugabannin kananan hukumomin jihar 21, da su samar da matakan shawo kan matsalar yunwa ga jama’ar jihar.
Fintiri ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da majalisar shugabannin kananan hukumomin jihar suka ziyarci gidan gwamnatin jihar, domin su taya shi murnar nasarar da ya samu a kotun koli.
- AFCON: Mai Yi Wa Kasa Hidima Ya Rasu Yayin Kallon Wasan Nijeriya Da Afrika Ta Kudu A Adamawa
- Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari -Fintiri
Gwamnan ya roki shugabannin kananan hukumomin da cewa bayan sun biya albashin ma’aikata su kuma tura wasu kudade da kayan aiki don samar da hanyoyin saukaka wa jama’a wahalar rayuwa da ake ciki.
Ya ce ya kamata shugabannin kananan hukumomin su lura da wuraren da ya kamata su ba jama’a agaji, kamar fannin kiwon lafiya da sufuri da abinci.
Gwamnan ya ce, ya lura da mafi munin rashin tsaro da ke addabar Nijeriya da duniya a zahirin gaskiya shi ne yunwa da wahala da hauhawar farashin kayayyaki, don haka akwai bukatar a samar da tallafi ga jama’ar jihar ta hanyar shugabanci na gari.
Gwamnan ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta rubanya kokarinta na ganin ta samar da wasu hanyoyin da za su rage wahalhalun da jama’a ke ciki a jihar.
Da yake magana tun da farko shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa (ALGON) reshen jihar, Alhaji Abdussalam Gidado, ya taya gwamna Fintiri murnar sake lashe zabe a karo na biyu da kotun koli ta tabbatar, ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba shi goyon baya domin ci gaban jihar.