Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad Abdulkadir, ya umarci al’ummomin fadin jihar da suke fitowa su yaki masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’addan da suke yankunansu.
“Yau bana kunya a gaban kwamishinan ‘yansandan na ce duk wanda ya taba ku zai kashe ku, ku kashe shi. A matsayina na Babban Jami’in Tsaron jihar nan duk wanda ya taba ku kar ma ku yi wani shayi ni na ce a kashe shi.”
- Dan Wasan Duniya, Pele, Ya Rasu Yana Da Shekaru 82
- An Gurfanar Da Matashi A Kotu Sakamakon Lakadawa Dan Sanda Dukan Kawo Wuka
Gwamnan, ya ce gwamnatinsa ba ta da wani mafita da ya wuce kawai ta ba da wannan umarnin domin masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga suna ci gaba da tafka ta’asarsu na kashe mazauna jihar da ba su ji basu gani ba.
Gwamnan ya ba da wannan umarnin ne biyo bayan hare-haren baya-bayan nan da aka kai wasu kauyuka tare da kashe mutane sama da 20 a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.
Muhammad, ya yi wannan umarnin ne a yau Alhamis yayin ziyarar kauyukan Rimi, Mansur, Yalwan Duguri dukka da suke karamar hukumar Alkaleri domin jajanta musu kan hare-haren ‘yan bindiga.
“Kuma wadannan mutanen da suka taba ku mu ma mun taba su kuma da ku muka taba su, mu ba a sanmu ragayewa ba. Duk wanda ya ce mana kule za mu ce masa cas a kasar Duguri, mun sha wahala saboda rashin rayuka da dukiya. Amma na ji dadi yadda kuka fito kuka kare hakkinku.
“Saboda haka ku fito ku yi na ranku ku fito ku yi yaki, mu ba a sanmu a ragonta ba, ba wai daga Zamfara ba, ko daga birnin Sin mutum ya fito ba za mu bar shi ba.
“Da wanda ya ke bada labari ga ‘yan bindigan nan ku fito da shi ku kawowashi wurin ‘yansanda a hukunta shi domin babu mugun mutum kamar Infoma kuma a cikinmu suke.”
A bangarensa kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Aminu Alhassan, ya shaida cewar gaggawar kai dauki ga wadanda ‘yan bindiga suka kawo hari na matukar taimakawa wajen dakile aniyar ‘yan ta’adda a jihar.