Daga Muhammad A. Abubakar
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta yi kira ga manyan jami’anta da su koma gona domin su samu habbaka a tattalin arzikinsu, wanda kuma gonar ce za ta haifar da haka, ba wai kawai bisa dogaro da aikinsu ba.
Marshal Boboye Oyeyemi ne ya bada wannan shawarar a wani taro da ma’aikatar noma da ci gaban karkara ta shiryawa manyan Jami’an hukumar Kiyaye hadurran a ranar Talata 19 ga watan Satumbar 2017, a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Mr. Oyeyemi, ya jinjinawa gwamnatin tarayya bisa kokarinta na bunkasa harkar noma, inda ya ce; “Shiga harkar noma wani al’amari ne da yake bayar da damar samun shiryawa ingantaccen rayuwa. Sannan ya bayyana cewa; “wannan sabon dabara da gwamnati ta zo da shi, za mu shiga domin a dama damu. Wannan wata dama ce da Ministan noma, Cif Audu Ogbeh ya bamu.”
Ya ci gaba da cewa; “wannan dama ce ta shiryawa rayuwar gaba, kuma wani tagomashi da gwamnatin tarayya ta yi mana, shi ne na bamu damar shiga harkar noma. Babban abin farin cikin shi ne yadda gwamnati ta yadda da wannan, kuma gwamnatin za ta karfafa mu domin tuni ta hadamu da Bankin Manoma don jami’anmu su fara karbar basussuka.”
Har wala yau, ya shawarci jami’an nasa da cewa; “Kada ku jira har sai kun samu babbar gona, za ku iya farawa da karama. Dama ni can manomi ne. Idan ku ka shiryawa rayuwarku da kyau, ba za ku taba kasancewa cikin damuwa a rayuwar gobe ba.”
Tunda farko, sai da Ministan Noma, Cif Audu Ogbe ya tabbatarwa da manyan Jami’an hukumar cewa: gwamnati za ta tallafa da horo da taimako ga duk wanda ya ke da sha’awa a bangaren harkar noma.
Muyiwa Azeez wanda shi ne Daraktan bangaren kasuwancin noma da gudanarwa na hukumar Noman, shi ne wanda ya wakilci ministan noman.
Ministan ya jaddada cewa; taimakon da za su bai wa Jami’an zai hada da na kayan gona, shawarwari da kuma yadda za su yi kasuwancin noman na su.
Babban mashawarci ga Ministan kan ayyuka na musamman da ayyukan bai daya, Winfred Ochinyabo, ta ce; babban kalubalen da gwamnati ta ke fuskanta a shirinta wanda ta tanada wajen bunkasa harkar noma shi ne yadda ake samun rashin wadatar abincin da ake bukata da kuma wadanda za a iya fitarwa zuwa waje.
Mrs. Ochinyabo ta ce; hada hannu guda akan wannan shirin shi ne zai kawo karshen matsalar karancin abinci da ake fama da shi a kasar nan.
“Dole mu budd wata hanya ta samar da hanyar shigar kudi a harkar noma, ba kawai tunanin ciyarwa ba. Kuma hukumar kiyaye hadurra za ta iya tabbatar da wannan. Domin duk zamu iya kasancewa wajen yin noman a matsayin kasuwanci.”
Taron wanda aka yiwa take da; “Wadatar abinci wajen tabbatar da tsaron kasa,” an fara shi ne a ranar 13 ga watan Satumba tare da rundunar Sojan Sama, Jami’an gidajen Yari ta kasa, da kuma wasu jami’an hukumar kiyaye gobara ta kasa. Har wala yau za a shirya irin wannan taron ga rundunar Sojan Nijeriya, Hukumar fasa kwauri ta kasa, da sauran hukumomin tsaro na Nijeriya.