Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ku Rungumi Noma – Gwamna Bala Ga ‘Yan Siyasar Bauchi

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya umarci dukkam masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa da su rumgumi aikin noma gadan-gadan domin wanzar da juyin juya hali a wannan fanni na rayuwa.

Gwamna Bala Muhammad ya bayar da wannan umarni ne a garin Bauchi a karfen mako lokacin da yake kaddamar da kasuwar sayar da takin-zamani na wannan damina da muka shigo domin wadatar da jihar dama kasa baki daya.
Ya ce, “Domin zurfafa aiyukan naduke tsohon ciniki tsakanin ‘yan-boko, na umarci ma’aikatar aikin gona ta jihar Bauchi ta tabbatar da cewar, dukkan ‘ya’yan majalisar gudanarwa ta jiha su koma gona domin noma abinci da kayayyakin masarufi. Na sake jaddada wa cewar, lalle ne kowane mai rike da mukamin siyasa a wannan gwamnati ya noma a takaice hekta daya na gona”
Gwamnan ya ce, “Ba wata togiya tsakani na da wani, zan dauki fartanya na tafi gona domin ni ba ma’abucin yawace-yawace bane, ko tinkaho da zuwa Abuja, saboda babu wani abu dazan dauka a birnin Abuja.”
Ya kara da cewar, “Idanduna na a bude suke kan lamura, kuma ni mazaunin Bauchi ne. Abin fahari ne a ce na zauna a garin Bauchi har na tsawon watanni uku, ba tare da na je ko’ina ba, ko wani wuri daga garin Bauchi ba.”
Don haka, gwamna yayi kira ga daukacin ma’aikatan gwamnatin jihar nan da su yi koyi da irin dabi’ar tasa, yana mai nusar da ma’aikata da su himmatu wajen tafiyar da aikace-aikacen gwamnati, la’akari da nauye-nauyen da jama’a suka dora masu su.
Bala ya shaidawa taron bikin kaddamar da kasuwar cinikin takin cewar, “Muna fadi-tashin ganin cewar, mun sauke nauye-nauyen da jama’ar jihar mu suka dora mana, ba tare da yin wasa da wannan nauyi ba. Ya zama wajibi a garemu, mu duba da idon basira, saboda gani ya kori ji, kuma daga na gaba ne ake gane zurfin ruwa”.
“Zan tanadi gona. Kazalika nasan mataimaki na ma manomi ne, saboda shike rike da sarautar sarkin aiyuka a masarautar Bauchi, shi ma kamar Bako da Tukura ne, duk Umbutawa ne”, Inji gwamna.
Daga nan, sai gwamna yayi alkawari wa kansa na dubawa da tabbatar da ambi wannan umarni nasa na jama’a su koma gona, yana mai cewar, “Matukar mun nuna misali, sauran manoma zasu yi koyi, wanda zai sanya daukacin al’umma su goya baya.”
Bala, wanda yayi tir da halayyar wasu mutane a baya, inda ya kasance Taki da aka yi nufin jama’ar Bauchi da shi, ake karkatar da shi zuwa kasuwa saboda son zuciya, sai yayi gargadi da cewar, gwamnatinsa ba zata lamunci ire-iren wadannan halaya ba.
Ya ce, “Halayen mu kusan guda ne, kuma duk mun amince da hakan, kuma wadannan halaye basu wuce na tabbatar da cewa mun yi noma, kuma mun tabbatar da cewa wasu sun yi koyi damu wajen aiyukan noma”.
Ya kuma bayyana cewar, ana ta bibiyar tsare-tsaren aiyukan gona da ake dauke dasu, domin ganin cewar, manoma sun juya akalar sana’ar tasu ya zuwa ta kasuwanci da zata samar da abin hannu.
Bala ya ce, ziyara da ya kai kasar Jamus a kwanakin baya, ta bashi nasarar tattaro masu zuwa zuba jari wa jihar ta Bauchi, yana mai cewar, akwai kwarin gwuiwa na kamfanoni da yawa zasu zuba jarinsu a bangaren noma a Bauchi da zummar kambama tattalin jama’a fiye da yadda Man fetur zai yi.
Sanata Bala Muhammad ya sanar da cewar, gwamnati zata sayar da takin NPK kan kudi naira dubu biyar (N5, 000), kazalika takin Urea dubu bakwai, (N7, 000) ba kamar yadda ake sayar da shi a kasuwa ba na kudi naira dubu takwas (N8, 000).
Daga cikin abubuwan da suka wakana a wajen bikin sun hada da baje kolin kayayyakin noma da kiwo da jihar Bauchi ke sarrafawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: