Matar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu a ranar Laraba ta ce, tikitin Musulmi da Musulmi ya bude wani sabon salo kuma sabon babi a siyasar kasar nan a 2023.
Da take buga misali da tikitin Shugaban kasa na musulmai biyu a jam’iyyar APC da yadda hakan ke cigaba da janyo cece-kuce, matar na Tinubu ta yi fatan cewa nan gaba kuma wata rana sai an samu tikitin Kirista da Kirista biyu a kasar nan.
Kan hakan ne ta ce ga masu daga jijiyar wuya kan hakan da su sha kuruminsu yanzu an bude babi ne don kuwa wata rana za a samu tikitin Kirista biyu.
Ta yi wannan harsashen ne a yayin gangamin kamfen din APC na Mata a shiyyar Kudu Maso Yamma da ya gudana a Mobolaji Johnson Arena a Legas.
“Dangane da tikitin musulmai biyu, wannan ya bude wani sabon fage a siyasar kasar nan, kuma nan gaba za a sake samun wani makamancinsa. Wani lokaci a nan gaba za mu samu tikitin Kirista da Kirista.”
Ta mika godiyarta ga uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari wacce aka tura wa katin gayyata amma ba ta samu halartar ba.
“Muna mika muku godiya bisa fitowa da kuka yi kuka halarci wannan taron. Zuwa na nan kamar zuwa gida ziyara ne. A shekaru 23 da suka wuce, Allah ya albarkaci mijina ya zama gwamna, na ba shi goyon baya dari bisa dari a matsayina ta matar gwamna.”
Matar Tinubu din wacce ta misalta gangamin a matsayin ziyara zuwa gida “Ina kuma godiya ga al’ummar Legas ta tsakiya bisa turani Majalisar Dattawa domin na wakilcesu. Ni ne mace ta farko da ta zama Sanata har sau uku. Wannan babbar damace a gareni. Tun 2007 da mijina ya bar gwamna, na cigaba da aiki wa jama’anmu masu albarka.”
Matar gwamnan Jihar Legas, Dakta Ibijoke Sanwo-Olu, ta ce, Nijeriya na bukatar wani jajirtacce irin Tinubu wanda zai iya tafiyar da harkokin kasar nan a nan gaba.
Ta ce, Gwamnatin Tinubu za ta baiwa Mata damarmaki masu yawa.